Rundunar tsaron teku ta kasar Sin ta gabatar da wani bidiyo a daren jiya Laraba, wanda ya nuna yadda jirgin ruwa mai lamba 3003 na kasar Philippines ya matsa kusa da jirgin rundunar tsaron tekun na kasar Sin mai lamba 3302 bisa rashin kwarewa, har suka yi karo da juna. A wannan rana kuma, jirgin ruwa na rundunar tsaron teku na Philippines da jirgin ruwa mai gudanar da harkokin gwamnatin kasar da jiragen ruwan aikin su da dama sun shiga yankin teku na tsibirin Huangyan na kasar Sin ba bisa doka ba.
An lura cewa, a ran 8 ga watan Nuwamban da ya gabata, shugaban Philippines Ferdinand Marcos ya sa hannu kan wasu dokoki da suka hada da “Dokar yankin teku” da “Dokar hanyoyin jirgin ruwa a teku”, wadanda suka shigar da yankunan Sin kamarsu tsibirin Huangyan da yawancin yankin tsibiran Nansha da yankunan teku dake kewayensu cikin yankunan kasarsa ba bisa doka ba, da zummar tabbatar da haramtaccen hukuncin da ya yanke kan tekun kudancin Sin. Ba a cika wata daya da sanya wadannan dokokin ba, bangaren Philippines ya sake kutsa kai cikin tekun kudancin Sin, kuma burinsa shi tabbatar da haramtattun dokokin da ya zartas.
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Wadanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
- Afirka Ta Kudu Za Ta Fara Bai Wa ‘Yan Nijeriya Bizar Shekaru 5
Ban da wannan kuma, an lura cewa, a karshen watan Nuwamban da ya gabata, a karon farko Amurka ta amince da jibge wata rundunar sojinta a Philippines da aka kira da “Rundunar soja ta musamman na sashen tudun ruwa na Ren’ai Jiao”. Matakin da ya zuga Phlippines ta dauki matakai yadda take so a tekun don cimma moriyarta.
Sin tana tsayawa tsayin daka kan warware rikicin tekun kudancin kasar ta hanyar shawarwari, da ci gaba da kiyaye cikakken ikonta na mallakar yankunanta da tekunanta ba tare da tangarda ba. Amma Philippines ta rika tada rikice-rikice ba iyaka, sai dai, munafuncin dodo ne ya kan ci mai shi. Kasashen da ba ruwansu kan wannan batu, wadanda suke zuga ta, ba za su dakatar da kokarin kasar Sin na tabbatar da hakkinta ba ko kadan. (Amina Xu)