An fara shirye-shiryen mayar da dakin otal din da Lionel Messi, ya zauna lokacin da aka yi Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar wajen tarihi.
Messi dai ya jagoranci Argentina wajen lashe kofin duniya, bayan da ta lashe gasar 1986, bayan doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
- Bolanle Raheem: Sufeton ‘Yansanda Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da ASP Drambi Vandi
- Babu Hannunmu Wajen Murdewa Kowa Zabe – INEC
Messi mai shekaru 35 ya lashe gasar a karon farko a tarihin rayuwarsa.
Dan wasan dai a iya cewa ya zama gagara badau, inda ya lashe kusan kowace gasa da ya taba bugawa a rayuwarsa.
Dakin dai za a mayar da shi wajen tarihi idan magoya baya za su koma kallon wajen da zakaran na duniya ya dinga kwana.
Argentina dai ra fara gasar ne da rashin nasara da ci 2-1 a hannun Kasar Saudiyya.
Sai dai tun daga wannan rashin nasara ba ta sake rashin nasara ba har zuwa lokacin da ta lashe gasar.