Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya ce samun kyakkyawar duniyar bil adama ta gobe, ya ta’allaka ne ga tabbatar da daidaito a dangantakar Sin da Amurka. Qin Gang ya bayyana hakan ne cikin wata makala da ya sanyawa hannu, aka kuma wallafa ta a jaridar Washington Post ta ranar Laraba.
Cikin makalar tasa, Qin ya ce kafin nada shi ministan harkokin wajen kasar Sin a karshen shekarar da ta gabata, ya rike mukamin jakadan Sin a kasar Amurka tun daga watan Yulin 2021, ya kuma lura da muhimman abubuwa da suka faru, da suka tsaya masa a tunani game da kasar Amurka. Ya kuma koma gida kasar Sin a farkon makon nan domin fara aiki a sabon mukamin nasa.
Ya ce “Na bar Amurka da gamsuwar cewa, har kullum kofar raya dangantakar Sin da Amurka a bude take, kuma ba za a taba rufe ta ba. Kaza lika na gamsu cewa, Amurkawa, kamar Sinawa, suna da zurfin tunani, da son jama’a da aiki tukuru. Don haka bai dace mu bari kyama ko rashin fahimtar juna, su kunna wutar fito-na-fito, ko haifar da tashin hankali tsakanin al’ummun sassan biyu ba. Ya kamata mu bi muhimman tsare tsaren da shugabannin kasashen mu suka amincewa, tare da zakulo managartan hanyoyin samun jituwa da juna, domin wanzar da ci gaban duniya baki daya”. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp