A yau Jumma’a ne aka kaddamar da taron tattauna mai taken “zamanintarwa iri ta Sin da duniya”, a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya bayyana cewa, tabbatar da zamanintawa, hakki ne na ko wace kasa, wanda ba za a iya kwace mata ba, kuma ba hakkin musamman ne na wasu kasashe kalilan ba.
Game da sauran maganganu marasa tushe da aka baza, cewa wai “Kasar Sin tamkar barazana ce ga tsarin kasa da kasa”, ko “Kasar Sin tana yunkurin canja yanayin tekun Taiwan da karfin tuwo”, ko kuma “Kasar Sin tana gurgunta kwanciyar hankali a tekun Taiwan”, Qin Gang ya jaddada cewa, wadanda ke lalata kwanciyar hankalin tekun Taiwan, su ne masu neman ‘yancin kan Taiwan, da wasu kasashen dake mara musu baya, kuma ba zai yiwu a taba raba yankunan kasar Sin ba. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp