Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta shaidawa manema labarai a yau Talata cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, zai gana da takwarorinsa na kasashen yankin tsakiyar Asiya, a gun taron ministocin Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na 4 da za a kira a birnin Xi’an dake lardin Shaanxi.
Taron dai zai hallara firaministoci, ko ministocin harkokin waje, da manyan jami’ai daga Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan, da Uzbekistan da dai sauransu.
Yayin taron manema labaran na yau, wani dan jarida ya yi tsokaci kan yadda a kwanan baya, gwamnatin Habasha ta gudanar da babban taron yabawa kokarin da ake yi a fannin shimfida zaman lafiya, a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar, har ma manzon musamman na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da harkokin kahon Afrika Xue Bing ya halarci taron, tare da karbar takardar yabo, wadda firaminitan kasar Abiy Ahmed Ali ya ba shi.
Don gane da hakan, Mao Ning ta ce Sin na nacewa ga goyon bayan gwamnatin Habasha, wajen kiyaye ikon mulkin kai, da cikakkun yankunan ta.
A sa’i daya kuma, tana yin iyakacin kokari wajen ingiza shawarwari cikin lumana. Ta ce Xue Bing ya nuna himma da gwazo, wajen tabbatar da wannan aiki, wanda ya taka rawa mai muhimmi, tare da kasashe dake wannan yanki, ciki har da Habasha, ta yadda za su tabbatar da tunanin wanzar da zaman lafiya a kahon Afirka.
A cewar Mao Ning, baiwa Xue Bing lambar yabon na nuni ga yadda Habasha ta fahimci kokarin da Sin take yi.
Kaza lika, Mao Ning ta ce, ya zuwa yanzu, an kwashe yawancin jama’ar Sin daga Sudan, zuwa tashoshin jirgin ruwa dake kan iyakokin kasar da kasashe makwabtanta, inda za a tsugunar da su yadda ya kamata. (Amina Xu)