Wasu daga cikin ‘yan takara a jam’iyyar PDP, SDP, PRP a Kano sun bayyana ra’ayoyinsu kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) karkashin shugabancin Ambasada Abdullahi Zango, ta gabatar da zaben ta a Kano.
Shugaban matasa na jam’iyyar PDP, Hon Salisu Dani ya ce yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsara na hana ba da kudi domin a zabi mutum ya yi daidai. Ya ce hakan ne zai sa a samu dimokuradiyya mai tsafta a Nijeriya.
Dan takarar majalisa a PDP, Hon Rabiu Sale Wangal ya ce wannan ya ba su kwarin giwar yin nasara a zaban.
Shi kuwa, tsohun ma’aji a jam’iyyar APC kuma dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar SDP, Hon Bala Muhammad Gwagwarwa ya ce duk abin da za a yi a tsaya kan gaskiya kuma a bi a hankali domin babu wani abu da zai tafi daidai ba tare da kwatatanta gaskiya ba, kuma akwai bukatar tsarin da zai amfani al’umar kasa a matakan kananan hukumomi ta hanyar ba su kudadansu daga gwamnatin tarayya kai-tsaye yadda za a iya rage matsaloli da talauci.
A nasa bangaren, shugaban jam’iyyar PRP na Kano, Injiniya Abba Namatazo ya ce zaban da hukumar INEC ta gabatar a kasa baki daya su dai sun gamsu da yadda hukumar ta gabatar da zabe, amma rashin nasarar PRP ta samu ne sakamakon goguwan sauyi a siyasance.
Ya ce a baya an yi guguwar PRP, inda aka zabi jam’iyyar a Kano a shekarar 1979, sannan kuma an samu guguwar jam’iyyar APC a 2015 da 2019, kuma wata rana za a dawo a sake yin PRP.