A wannan fili namu a wannan makon mun ji ra’ayoyinku ne a kan kiraye-kirayen da wasu ‘yan Nijeriya ke yi na neman a kafa Gwamnatin Rikon Kwarya, shin hakan zai haifar da da mai ido kuwa?
Nuruddeen Muhammad Funtua
Aslm to gaskiya kafa gwabnatin rikon kwarya ba ita ce mafita ba mu dai kawai kamata ya yi a gyara harkar dabe wanda talakawa suka daba ko ince al’umma abasu shi ne mafita muna rokon Allah ya tausaya mana ya ba mu shugabanni nagari wanda za su taimaka mana albarka annabin mu s.a.w.
Kabo Idris Saminu
Gwamnatim rikon kwarya ba za ta haifar da da mai ido ba sabila da kuwa shine duk abin da za’a yu muddin ba za’a mutinta sha’anin talaka ba gaskiya babu inda abun nan zai je fatan dai kawai ko mene ne a duba bukatun talaka shine kawai a inganta rayuwa.
Engr Abdullahi Musbahu Dambatta
Gaskiya gwamnatim rikon kwarya ba za ta haifar da da mai ido mudai fatan mu allah ya kyauta Allah kuma ya shiga lamuran mu
Hadiza Bello Hamza
Bai kamata ana irin wannan maganan ba, musamman ganin an gudanar da zabe, an kuma samu wadanda suka lashe, ai sai a basu ragamar shugabancin suma su gwada nasu fasahar. Allah ya jagoranci kasata Nijeriya
Ahmad Dan Maryam
Bana goyon bayan kafa gwamnatin rikon kwarya, tabbas bga zai haifar da da mai id oba. Ana kafa Gwamnatin rikon kwarya ne in aka samu yamutsi da tashin hankali a yayin da aka yi zabe amma a wannan lokacin an gudanar da sahihin zabe, me ya kawo maganar gwamnatin rikon kwarya?
Farida Usman
Ina kira ga dattawan Nijeriya da su hada hannu su yaki wannan shiri na neman kafa gwamnatin rikon kwarya don ba alhairi ba ne ga al’ummar Nijeriya. Ya kamata a ba kowanne bangare na Nijeriya damar mulki don kowa ya san ana yi da shi.