A yau mun kawo muku ra’ayoyin masu karatun mune a kan halin da ake ciki a yankunan su bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake fuskanta a wasu jihohin Arewacin Nijeriya a ‘yan kwanakin nan.
Ibrahim Hassan Baban Adila
Gaskiya bana kam a garin Gombe mun samu ambaliyar ruwan sama musamman a yankin kananan hukumomin Jihar Gombe irin su Bajoga da Kwami da sauransu sai dai matsalar gwamnati ta yi ko inkula da su gaskiya, daga karshe muna kira da gwamnoni dasu dubi lamarin don kawo gyara tara da bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.
Sakodaga ibrahim Hassan Minister Abban Adila da Ansar jihar Gombe.
It’z Sam Dambatta
To mu dai anan yankinmu Alhmdulillah domin cikin ikon Allah da rushewar gidaje ko ambaliyar ruwa duk da sauki a wannan yankin namu. Muna kara gode wa Allah da wannan ni’ima
Umar Ibrahim Umar
Alhamdulillah gaskiya dai damunar bana ba’a cewa komai sai dai addu’a Allah ya bamu wucewa lafiya wanda ta yi sanadiyar rasuwarsu Allah ya karbi shahadarsu wanda suka yi asarar dukiya kuma Allah ya mayar musu da alheri, Amin
It’z Jameel Moh’d
Masha Allah, a nan jihar Taraba mu dai alhmdullah sai dai mu yi adu’ar fatan zaman lafiya mu girbe abinda muka shuga lafiya cikin kwanciyar hankali
Adamu Yunusa Ibrahim
Inda mu ke kam babu wata matsala. Alhamdulillah
Rah’iss Abba Lawan
Mu kam Alhamdulillahi bamu da matsala da ruwan sama
Abdulmumini Sese
Har mun fara girbi
Isma’il Hussain Musa
Mu kam sai godiya, Allah ya kara mana lafiya
Nuruddeen Muhammad Funtua
Ina fatan alkhairi a gareku baki daya yan uwa da abokan arziki. Mudai a namu yanki sai dai godiya ga Allah madaukakin Sarki, ruwa kam ba a cewa komai, muna adu’ar Allah ya sa muga karshen ruwan lafiya, ya bamu damina mai albarka
Sani Ladan
Mudai kam a namu yanki sai godiya domin amfanin gonakinmu na kara kyau, muna fatan girbi mai kyau sakamakon wadataccen ruwan sama amma duk da haka ba a rasa asarar gine-gine ba Allah ya bamu alkhairan da ke cikin wannan damina
Engr Abdullahi Musbahu Dambatta
Fatan mu shi ne ubangiji ya bamu mai albarka wanda kuma za mu iya sarrafawa
Yusuf Muhammad Jalingo
Mu a namu yankin (Gombe) sai godiya saboda wasu wuraren kamar su Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye an samu asarar rayuka da dukiyar al’umma. Haka a jiya ma an sami yankewar wani hanya a wassu wuraren sai dai a kwaryar jiha abin da sauki kadan. Muna jan hankulan ‘yan uwa ake kulawa da magudanan ruwa saboda gujewa ambaliya, Allah ya bamu damuna mai albarka. Amiin
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
A gaskiya mu a Katsina Alhamdu-lillah, ana samun ruwa sosai sosai. Sannan kuma dai akwai saukin ambaliyar ruwa, kuma gidaje ba su cika rushewa kamar shekarun baya. Allah ka ba mu damina mai albarka ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Shamsi Umar Bakanike Dambatta
Tabbas a wannan mako and akko maudu’i mai matukar muhimmachi duba da yadda aka sha ruwa kamar da bakin kwarya, toh muma dai anan karamar hukumar Dambatta haka abin yake kamar yadda aka sha mamakon wannan ruwa a wurare daban-daban sai dai mu anan karamar hukumar Dambatta an sami rugujewar gine-gine domin kuwa a wasu yankin ma na karamar hukumar Dambatta hadda asarar rai da aka samu dama asarar dukiya da fatan dai Allah yajikan wanda suka rasu ya kuma kiyaye faruwar hakan anan gaba.