Kwanakin baya ne Ministan Kwadago Dakta Chris Ingige ya sanar da cewa, gwamantin tarayya ta fara shirye-shiryen ganin an kara wa ma’aikatan gwamnatin tarayya alawus don ya yi daidai da yadda ake samun hauhawar farashinn kayyakin masarufi. Shin hakan zai rage radadin matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayan masarufi da ake fama da shi? Ga dai yadda masu bibiyarmu suka bayyana nasu ra’ayinsu.
Mohammed Inuwa
Zai taimaka matuka in aka lura da yadda ma’aikatan ke cikin wani hali saboda tsadar kayayyakin masarufi da kuma tsadar rayuwa da ake ciki. Kuma yakamata gwamnati ta kawo hukumar kula da daidaiton farashin kayan masarufi, kuma ta bude wasu wajajen sayar wa talakawa kayan masarufi mai sauki domin taimakonsu. Nagode.
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya na ji dadin haka saboda tsadar kayan yau da gobe, insha Allah zai rage radadin hakan alfarmar Shugaba (s.a.w.)
Sani Ladan
A a ba zai rage radadi da matsalar hauhawar kaya ba sai dai ma ya karu domin idan kace gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikatanta karin albashi kuma bata kayyade farashin kaya ba lallai ‘yan kasuwa sun sami hanyar yi wa kayansu karin kudi yadda suka ga dama, amma abinda yafi dacewa gwamnati ta yi shi ne kayyade farashin kayan masarufi wannan ita ce hanyar farko ta nemawa ma’aikata saukin rayuwa amma ba karin albashi ba koda za ta yi karin to ya zama ta kula da farashin kaya, muna rokon Allah ya kawo mana sauki a rayuwar mu.
Kabo Idris Saminu
A gaskiya wannan ba zai rage ba domin ai an yi a baya kuma ba a ga wani canji ba abin da gwamnati ya dace ta yi shi ne ta daidai ta farashi shi ne kawai ba wai karin albashi ba da a kasar babu tsayayen farashi kullum sai hauhawa yake yi.
Real Miftahu Ahmad Panda
A’a, ba na tsammanin yin karin albashi ga ma’aikata, zai kawo karshen halin matsin tattalin arziki, ko hauhawar farashin da mu ke tsaka da fama da ita, a kasar nan, duba da cewar, a duk lokacin da aka yi batun za a kara wa Ma’aikata albashi, muna ganin yadda farashin kayayyaki su ke ninninkawa, tun ma kafin a yi karin, hakan ya kansa ko da bayan an yi, sai a rasa a ina alfanun da ake tsammanin samu ya makale.
Ni a ganina, daukar matakan da za su daga darajar takardar kudi ta Naira, shi yafi muhimmanci, a kan yin karin Albashin, duba da yadda tattalin arzikin mu ya dogara da Dalar Amurka, ina ganin idan aka farfado da darajar Naira, to tabbas komai zai yi sauki.
Abdul’aziz Mohammed
Muna muku barka da warhaka. A gskiya ata wanii fannin hakan abin a yaba ne zai iya kawo saukin rayuwa kadan amma ga ma’aikatan gwamnatin tarayya, saboda idan muka duba karin da aka yi a baya na naira dubu 30 har yandu wasu jihohi da dama sun kasa aiwatar dashi.
Abin yi babba ga gwamnatin tarayya shi ne ta yi kokarin kawo tsare tsare da tabbatar dasu wanda zai tabbatar da rage hau_hau kayan masarufi. Allah ya taimaki kasar mu Nijeriya ameen.
Comr Hassan S Umar
Toh gaskiya dai abin lura a nan shi ne a duk lokacin da aka samu karin albashi idan ka tsaya zaka ji tashin kayan masarufi ya biyo baya, karshe karin da za a samu sai ya wuce abin da gwamnati takara a albashin ma’aikata.