A wannan makon mmun kawo muku ra’ayoyin al’umma ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan murnar bikin zagayowar ranar haihuwar Annabin Tsira, Muhammadu Bin Abdullah (SAW). Ga dai yadda suka tofa albarkacin bakin su
Comr Hassan S Umar
Alhamdulilahi, bukukuwa sun tafi yadda yakamata, Haka a fadin karamar hukumata ta Minjibir a Jihar Kano bana ma munata shagulgula.
Abubakar Ghali
To alhamdulillah gaskiya a wajejen mu Maulud ba kamar shekarar data gabata ba saboda matsalar tattalin arziki, amma muna godiya don ana ta bukukuwa du da maysion da ake fuskanta, Allah ya maimata mana
Omar Naseer Imam
Alhamdulillah, fatan mu zama masu yi don Allah, Allah ya ba mu ladan ayyukan da muka gabatar
It’z Jameel Moh’d
Alhamdulilah, muna godiya kwarai da gaske da muka samu kan mu a cikin masu murnar haihuwar fiyayyen halitta (SAW). Happy Maulud.
Umar A Musa
Alhamdulilah, Allah Ya maimaita mana
Abdulmumini Sese
Maulud sa godiya
Umar Babagoro Dukku
Masha Allahu, Allah ya kara wa Annabi daraja
Murabbi Umar Muhammad
Labbaika Ya Rasurullahi
Murabbi Umar Muhammad
Allahumma Salli’alah Muhammad Wa’ali Muhammad.
Mamansadauki Rabi Atu Muhd
Masha Allah allahumma sali ala Muhammad wa Ali muhammad
Aliyu Ilyas Yusif
Allah ya kara wa Annabi daraja
Abubakar Infaki
Allah ya maimaita mana, amin summa amin.
Fafaalzazaal Rabiu Kano
Alhamdulilah, Allah ya kara wa Annabi daraja, amin
Hadiza Bello Hamza
Lallai mun sha biukukuwa, muna addu’ar Allah ya maimaita mana na badin badada
Lukman Alfah
A kullum Maulud sai kara karbuwa yake yi, mu kam mun yi bukukuwa yadda ya kamata
Akeela Murtala
Alhamdulilah, Allah ya maimaita mana wannan babbar ranar.
Zahara Murtala
Bukukuwan Maulud na wannan shekarar ya yi armashi, Allah ya maimaita mana