Kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Augustine Eguaevon ya gayyaci kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Rabiu Ali domin wakiltar Nijeriya a wasannin ‘yan wasan gida na kasashen Afirka (CHAN).
Rabiu Ali wanda aka fi kira da Pele ya buga wa Nijeriya wasanni 18 a tarihi inda ya jefa kwallaye 5. Ya samu wannan gayyatar ne bayan haskakawa da yake yi a kakar wasanni ta bana.
Zuwa yanzu, ya jefa kwallaye 8 a raga a a gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL), hakan ta sa Eguaevon ya sanya rai akan gudunmawar da Ali Rabiu zai iya bai wa tawagar Nijeriya.