Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da yin karin albashin naira dubu goma-goma (N10,000) ga kowani ma’aikacin gwamnati a fadin jihar domin rage radadi da matsatsin cire tallafin Mai.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Gombe ranar Juma’a, mataimain gwamnan jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya ce, wannan wani bari ne na cikin matakan da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke dauka na rage wa ma’aikata matsatsin tattalin arziki da ake ciki sakamakon cire tallafin na mai.
Ya ce, gwamna Inuwa Yahaya ya maida hankali sosai kan tabbatar da walwala da jin dadin ma’aikata tare da al’ummar jihar ta hanyar shirye-shirye masu dama kuma masu fa’ida tun lokacin barkewar annobar Korana.
Ya kara da cewa tun lokacin da aka zare tallafin mai, gwamnatin jihar take ta daukan matakai da bijiro da tsare-tsaren da za su taimaka wa jama’a wajen rage musu kaifin matsatsi da shiga takura a sakamakon hakan.
Ya kara da cewa, daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka har da raba tallafin naira dubu talatin-talatin (N30,000) wa mutum 420 000 a sassan jihar.
A fadin nasa, wannan karin albashin dubu 10 zai shafi dukkanin ma’aikatan gwamnati na jiha da na kananan hukumomi kuma zai fara aiki ne daga watan Agustan 2023.
Da aka tambayeshi kan zuwa yaushe ne karin zai tsaya, sai ya ce, “Karin dubu 10 kan albashin ma’aikatan babu ranar tsaida shi a yanzu.”
Mataimakin gwamnan ya jinjina ya gudunmawar da ma’aikatan jihar ke bayarwa, ya misaltasu a matsayin injunan da suke taimaka wa gwamnati wajen tafiyar da shirye-shirye da manufofinta.
Jatau ya kuma roki ma’aikatan jihar da su cigaba da kasancewa masu biyayya wa doka da oda, kuma ya roki wadanda har zuwa yanzu ba su samu tallafi ba da cewa su kara hakuri kaso na zuwa kansu.
“Ina kira ga al’umma musamman wadanda har yanzu ba su samu tallafi ba da su kara hakuri, a bangarenmu za mu cigaba da kawo tsare-tsare da kusan kowa sai ya mora da dan abun da muke da shi a hannu,” ya tabbatar.