Kimanin ‘yan siyasa 200 a Nijeriya da jami’an tsaro sun mallaki kadarorin da suka kai na kusan dala biliyan daya (Naira tiriliyan 1.49) a kasar Dubai cikin shekara 20, in ji rahoton Jaridar Businessday.
Mata da ‘ya’yan ‘yan siyasa da alkalan kotu da manyan ma’aikatan gwamnati da ke cikin wannan lamari, sun tara kadarori 1,600 a wurare daban-daban da suka shahara a Dubai.
- An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla
- Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG
Wannan binciken ya fito fili ne a bangaren wani aiki mai suna ‘Dubai Unlocked,’ wanda wani bincike ne na tsawon watanni shida kan bunkasar kasuwancin Hadaddiyar Daular Larabawa karkashin jagorancin Hukumar Bayar da Rahoton Laifuka da Cin Hanci da Rashawa (OCCRP) tare da abokan huldar kafofin yada labarai sama da 70.
Jaridar Businessday ta samu kebabbun kundaye wanda ke ba da cikakken bayani game da duk kadarori da ‘yan Nijeriya suka mallaka a Dubai. Kiyasi ya nuna cewa kadarorin da ‘yan Nijeriya suka mallaka a Dubai sun kai na dala miliyan 997.79.
A shekarar 2020, kadarori 800 da aka kiyasta kudinsu ya kai dala miliyan 400 ne kawai aka gano ‘yan Nijeriya sun mallaka a cikin babban birnin kasuwanci na Dubai, amma yanzu hakan ya karu zuwa kusan dala biliyan 1 da kadarori 1,600 biyo bayan sabuwar fallasa ta kididdigar kadarorin ‘yan Nijeriya da ke Dubai.
‘Yan Nijeriya su ne na biyu wajen sayen kadarori a Dubai bayan kasar Indiya, inda suka mallaki kadarori 1,824 a kasuwannin kasar, a cewar sashen jami’ai masu kula da kasa na Dubai. Ta hanyar nazarin bayanai, an gano cewa manyan jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati da mutanen da ke da alaka da gwamnati su ne suka mallaki kashi 88 na kadarorin ‘yan Nijeriya a Dubai.
ATIKU ABUBAKAR
Wani shahararren gida mai daki uku da aka kiyasta kudinsa ya kai dala miliyan 1.23 a Palm Tower da ke Dubai, mallakar Atiku Abubakar.
Diyar ATIKU Mai Shekaer 23
Wani gida mai daki daya a Cibiyar Kasuwanci ta Biyu da ke Dubai wanda kudinsa ya kai dala 104,135, mallakar diyar Atiku. Ta kuma mallaki wani gida mai daki biyu a Hadaek Sheikh Mohammed Bin Rashid wanda aka kiyasta kudinsa ya kai dala 289,305.75.
LATEEF FAGBEMI
Babban lauyan Nijeriya kuma ministan shari’a ya mallaki kadar wanda kydinsa ya kai dala 85,846 a Al Hebiah Third.
NASIR EL-RUFAI
Wani gida mai daki hudu wanda kudinsa ya kai dala 193,084 a Al Hebiah Third na an gano mallakar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rui ne.
YUSUF DATTI BABA-AHMED
Kadarori takwas da aka kiyasta kudinsu ya kai dala miliyan 2.28 an gano cewa mallakar abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LPa zaben 2023, Yusuf Datti Babba-Ahmed. Kaddarorin suna cikin zabbaun wurare kamar Burj Khalifa, Al Yelaiss, Al Barsha South Fourth, da Town Skuare Safi 2.
IFEANYI UBA
Wani kadara da aka kimanta kudinsa ya kai dala miliyan 1.13. Yayin da aka danganta kadarori takwas da matar Uchenna Uba. Ba a shigar da kudin kadarorin a cikin kudin ba, amma kadara daya a Wadi Al Safa 7 ta kai kusan dala miliyan 1.13, yayin da wasu biyu ke da kiminin dala $294, 516 kowanne su.
ATTAHIRU BAFARAWA
Kaddarori 7 da aka kiyasta kudinsu ya kai dala miliyan 1.48, mallakar tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ne, yayin da wani kadara ta gida da ke Palm Jumeirah kuma ya kai dala 750,112, mallakar matarsa ne.
AHMED MARKAFI
An gano wata kadara a Burj Khalifa da ta kai dala 822,016, mallakar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Marfi ne.
TAFA BALOGUN
Tsohon Sufeto-Janar na ‘yansandan, Tafa Balogun, wanda ya mutu, an alakanta shi da kadarori biyar a wurare daban-daban ciki har da Marsa na Dubai. Kaddarorin sun kai dala miliyan daya.
MBU JOSEPH
An gano wata kadara mallakar tsohon mataimakin sufeto-Janar na ‘yansanda, Mbu Joseph.
AHMADU ALI
An gano wata kadara da ba a bayyana kimanta ba mallakar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmadu Ali, yayin da daya da aka kiyasta kudinta ya kai dala 422,887 mallakar diyarsa, Khadijah Nneamaka Ali.
MAINA AJI LAWAN
An gano kadarori 11 mallakar tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Maina Aji Lawan
ASHE AHMADU MUAZU
Matar tsohon shugaban jam’iyyar PDP, ta mallaki wani kadara da ke Hadaek Sheikh Mohammed Bin Rashid, wanda kudinsa ya kai dala miliyan 1.16.
CHRISTABEL BENTU
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, ya mallaki wata kadara.
ISA MAHMOUD NUHU
An gano kadarori biyu mallakar babban jami’in hukumar kwastam ta Nijeriya (NIS), Isa Mahmoud Nuhu. An kiyasta kowacce kadara daya ta kai dala 553,802.
SALISU ABDULLAHI YUSHAU
An gano kadarori biyu na tsohon babban hafsan sojin saman Nijeriya, Salisu Abdullahi Yushau.
MOHAMMED SANI SIDI
Wani gida da ke Marsa Dubai, wanda darajarsa ta kai dala 590,807, an gano mallakar tsohon darakta-janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mohammed Sidi Sani, wanda aka kora a watan Afrilun 2023 tare da wasu daraktoci bakwai na hukumar. An kiyasta kudinsu zai kai dala 590,807.
HADIZA ALI SHERIFF
Wata kadara a Marsa Dubai da ta kai dala miliyan 3.093 ta kasance mallakar matar tsohon gwamnan Jihar Borno, Hadiza Ali Shariff.
NENADI USMAN
Wani gidaje a Dubai mallakar tsohuwar ministar kudi ta Nijeriya, Nenadi Usman.
BOBBOI KAIGAMA
An gano wata kadara mallakar shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Bobboi Kaigama.
JIMOH IBRAHIM
Sanata mai wakiltar Ondo ta kudu, Jimoh Ibrahim ya mallaki kadarori 7 a Dubai.
IKE EKWEREMADU
An gano kadarori biyar na Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda ke zaman gidan yari a kasar Ingila, Ike Ekweremadu.
ORJI UZOR KALU
An gano kadara daya na tsohon gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, wanda yanzu Sanata ne.
JEREMIAH USENI
An gano wata kadara ta tsohon gwamnan soja na tsohuwar Jihar Bendel, Jeremiar Useni.
OSITA CHIDOKA
Wani gida da aka kiyasta kudinsa ya kai dala 101,793.37 a Jabal Ali First ya kasance mallakar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka.
OLISA METUH
Wata kadara mallakar tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh.
ABDULSALAMI ABUBAKAR
An ce wani kadara a Marsa Dubai mallakin tsohon shugaban kasar Nijeriya ne, Abdulsalami Abubakar.
HASSAN ARDO TUKUR
Rahotanni sun bayyana cewa wata kadara da ta kai dala miliyan 1.025 mallakar tsohon babban sakataren tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne, Hassan Ardo Atukur.
ADEYEMI IKUFORIJI
An gano wata kadara a Marsa Dubai mallakar tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Legas, Adeyemi Ikuforiji.
DAN ETETE
Wani kadara mallakar Dan Etete (Dauzia Loya Etete), tsohon ministan man fetur na Nijeriya ne.
Binciken ya fayyace cewa bayyana sunayen da abubuwan da suka mallaka ba wani laifi ba ne domin babu wata shaida da ke nuna cewa sun mallaki kadarorin ne da kudaden sata. Har ila yau, bincike ya nuna cewa wasu ‘yan Nijeriya maza masu rajistar kadarorin sun sanya adireshinsu a matsayin ‘Puerto Rico’.
Haka zalika, an kuma yi wa wasu mazan Nijeriya rajista a matsayin mataye.
Baki sun mallaki kusan kashi 43 na kaddarorin gidaje a Dubai, in ji Hukumar Kula da Haraji ta EU. Yawancin kaddarorin sun samu izinin mallaka, ko da yake birnin yana ba da izinin mallakar kashi 100 cikin 100 a wurare masu zaman kansu da zarar an sami abokan tarayya na kasar.
Wasu manazarta sun ce tattalin arzikin Dubai yana habaka ne daga ‘yan Nijeriya da ke zuwa kasuwanci a kasar, wanda suka nuna damuwarsu. Sannan sun yi nuni da cewa dole ne Nijeriya ta dauki matakin da ya dace.
An kiyasta cewa kamfanonin gine-ginen gidaje a Nijeriya sun samu dala biliyan 13.2 (kashi 5.2) a farkon kwatan 2024, amma na Dubai ya ninka adadin sau 58.