Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da abin da ake kira wai “Rahoton ‘Yancin Addinai na Duniya na 2021” a ranar 2 ga watan Yuni, inda ta lissafa abubuwan da ake kira “laifi” na kasar Sin game da hanawa da take hakkin yin addini.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya gabatar da jawabi a taron bayar da rahoton, inda ya ci gaba da bata sunan manufofin kabilu da na addinai na kasar Sin.
Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Litinin cewa, girmamawa da kare ‘yancin bin addinai shi ne ainihin manufar addini ta jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar. Abubuwan dake da alaka da kasar Sin a cikin rahoton na Amurka, da kuma jawabin sakatare Blinken kan manufofin kasar Sin, sun yi watsi da gaskiya, kuma cike da kyamar akida, da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Kasar Sin ba ta gamsu da hakan ba, kuma tana adawa da hakan.
Kakakin ya yi nuni da cewa, ”Kisan kare dangi’ a jihar Xinjiang, karya ce ta wannan karni, wanda kasar Sin ta sha karyatawa bisa gaskiya da alkaluma.
Baku gaji da saurare ba, mun gaji da magana a kai. Dalilin da ya sa Amurka ta yi ta yada karairayi da ke da alaka da Xinjiang, Tibet da Hong Kong shi ne, kawai don neman fakewar batanci da murkushe kasar Sin, da kuma amfani da ita a matsayin wani makami wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da kuma raba kan kasar.”
Har ila yau, an ba da rahoton cewa, jami’an karamin ofishin jakadancin Amurka a Guangzhou, Sheila Carey da Andrew Chira, sun bayyana wa bakin a wata liyafa a shekarar 2021 cewa, gwamnatin Amurka tana fatan ‘yan kasuwan Amurka su fahimci cewa, yin amfani da jihar Xinjiang wajen yayata batutuwan na aikin tilastawa, kisan kare dangi, da kuma kai hari kan al’amuran kare hakkin bil’adama, “kokawa ce” kuma “hanya ce mai amfani.” Babban burin shi ne “shigar da gwamnatin kasar Sin cikin mawuyacin hali.”
Yayin da yake amsa tambaya game da wannan batun, kakakin ya ce, “Idan bayanan da ka ambata gaskiya ne, ba zan yi mamaki ba ko kadan, domin wannan ba shine karo na farko ba da jami’an Amurka suka ‘fadi a bayyane’. (Mai fassara: Bilkisu Xin)