Mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara kuma shugaban kwamitin ladaftar da ‘yan bindiga masu satar shanu da manyan laifuka Honarabul Sani Abdullahi ya tabbatar da cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da harkokin siyasa sakamakon ganin wasu ‘yan Boko Haram da ISWAP a sassan jihar.
Honabul Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai, ranar Talata a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A cewarsa, bayanan sirri da suka tattara sun tabbatar da cewa, kimanin ‘yan bindiga 1,200 ke shirin kai munanan hare-hare a jihar ta Zamfara, in ji Wanban Shinkafin.
An hango ‘yan Boko Haram da ISWAP a wani kauye da ake kira Mutu a gundumar Mada ta karamar hukumar Gusau a kan babura fiye da sittin, ana zarginsu da shirin kai munanan hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Wannane ta sa masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro suka nemi gwamna Matawalen Maradun ya dakatar da duk wasu tarurukan siyasa da rufe wasu hanyoyin garuruwa don ganin an dakile shirin ta’addancin.
Shinkafi ya kuma bayyana cewa, tsarin milkin tarayya ya bai wa gwamna ikon sa doka dan ceton rayuwar al’umma.
A cikin dokar ta 10, gwamnati ta dakatar da duk wasu harkokin siyasa a fadin jihar ta Zamfara.
A kan haka ne Wamban Shinkafi, ya yi Kira ga mutanan jihar Zamfara da su ci gaba da bai wa gwamnatin hadin kai wajan yaki da ‘yanbindiga suma ‘yan’uwanmu ‘yan siyasa da su bi dokar da gwamna ya sa wa hannu ta dakatar da harkokin siyasa, tunda akwai lokaci mai tsawo fiye da wata uku don jami’an tsaro su gama da ‘yanta’addan, in ji Wamban Shinkafin.