• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ramadan: Gwamna Dauda Ya Biya Ma’aikatan Zamfara Kuɗin Hutu Don Kyautata Walwalarsu

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da biyan ma’aikatan Jihar kuɗaɗen su na hutu a matsayin wata garaɓasa ta musamman albarkacin watan Ramadan.

A ranar Laraba ne ma’aikatan gwamnatin Jihar da na Ƙananan Hukumomi a Zamfara suka fara karɓar kuɗaɗen hutu.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ta bayyana cewa kuɗaɗen hutun ma’aikatan shi ne kashi 10 cikin 100 na albashin su na shekara.

A cewarsa, kuɗaɗen hutun da aka biya a matsayin kyautar azumin Ramadan wani shirin jin daɗi ne da aka bai wa dukkan ma’aikatan gwamnati domin sauƙaƙa wahalhalun tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Gwamna Lawal ta kasance mai son ma’aikata. “Bayan hawansa mulki, Gwamna Lawal ya biya duk albashin da ma’aikata ke bin gwamnatin da ta shuɗe, ya kuma biya kuɗaɗen garatuti, sannan ya amince da biyan albashin watanni 13 ga ma’aikatan jihar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

  • Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

“Saboda yanayin matsin tattalin arzikin da ƙasar nan ke ciki, Gwamna Lawal ya nuna jin daɗin sa da ƙwazon ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa. A matsayin sa na mai alheri, ya amince da biyan kuɗin hutu ga duk ma’aikata.

“Gwamnan ya jajirce wajen kyautata jin daɗin ma’aikatan gwamnati, tare da tabbatar da samun albashi da alawus a kan lokaci. Biyan kuɗin hutun wani alami ne na kulawar da Gwamnan ke nuna wa al’ummar Jihar Zamfara.

“Gwamnati ta riga ta biya kuɗaɗen hutu ga ma’aikatan Jiha da Ƙananan Hukumomi da ’yan fansho. Bugu da ƙari, masu riƙe da muƙaman siyasa, su ma sun samu garaɓasar kuɗin da zai taimaka musu a cikin watan Ramadan.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

October 16, 2025
Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

October 16, 2025
An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.