Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta bayar da umarnin rufe duk wajen shan barasa da wuraren karuwanci a cikin watan Ramadan.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan a ranar Talata a wata hira da ya yi da manema labarai.
- ‘Yan Siyasa Ne ke Kokarin Raba Kan ‘Yan Nijeriya —Solomon Dalong
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Adamawa
Ya ce matakin wani bangare ne na kokarin da hukumar ke yi na dakile munanan dabi’u a cikin watan Ramadan.
Dahiru ya bayyana cewa hukumar Hisbah ta gudanar da wayar da kan masu yin lalata da kuma masu sayar da barasa.
A cewarsa: “Mun zagaya irin wadannan yankuna a fadin jihar tare da gargadi ga masu aikata wannan aika-aika da su daina sana’arsu ta haram a cikin wannan wata na Ramadan ko kuma su bar jihar.”
Kwamandan Hisbah, ya bayyana cewa jami’ansu za su fara sintiri na gama-gari domin kame wadanda suka yi watsi da wannan umarnin hukumar.