Shugaba kasa, Bola Tinubu, ya bukaci masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma domin rage musu radadin da suke ciki musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Kano a lokacin da yake kaddamar da rabon shinkafa motoci 140 da Sanata Abdulaziz Yari ya bayar domin karrama shugaban kasa.
- Ramadan: Gwamnatin Sokoto Ta Amince A Biya Ma’aikata Da ‘Yan Fansho Kyautar Rabin Albashi
- Ramadan: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bayar Da Umarnin Rufe Duk Wani Gidan Gala Da Ke Kano
Tinubu wanda ya samu wakilcin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya kuma yaba da wannan karimcin.
Ya ce an yi hakan ne domin tallafa wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a wannan lokaci.
“A duk faɗin duniya, shugabanci na mutum fiye da ɗaya ne. A ko da yaushe akwai bukatar a taimaka wa marasa karfi a cikin al’umma.
Shugaban, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi addu’ar samun hadin kai da zaman lafiya da ci gaban kasar a cikin watan Ramadan.
Tun da farko, wakilin Yari, Dr Abubakar Danburam, ya ce manyan motocin 140 na dauke da buhunan shinkafa 50kg 84,000.
Danburam ya bayyana cewa za a raba kayan ga akalla magidanta 500,000 a Arewa.
Ya ce an yi hakan ne domin taimaka wa kokarin Tinubu na tallafawa mabukata da sauran marasa galihu a cikin al’umma.
Yari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi addu’a domin samun sauki daga kalubalen tattalin arzikin da ya dabaibaye Nijeriya.