Wasu tsirarun masu zanga-zangar a ranar Asabar sun fito kan titunan Kano, tare da bijirewa dokar hana fita da Gwamna Yusuf ya sanya a ranar Alhamis.Â
Masu zanga-zangar, da alluna, da suka taru a Mandawari da sassan yankin Nassarawa na Jihar Kano, suna rera wakokin, “Gwamna a kashe mu da harsashi da yunwa ta kashe mu.”
- Yadda Uwargida Za Ta Hada Miyar Uwaidu
- Amurka Za Ta Yi Amfani Da Fasahar Israila Don Kutsen Wayar Mai Yunkurin Halaka Trump
Zanga-zangar ta #EndBadGovernance don neman shugabanci nagari da inganta tattalin arziki ta shiga rana ta uku a ranar Asabar.
Zanga-zangar wadda ta fara cikin lumana a ranar Alhamis ta rikide zuwa rikici a Sani Mainagge, inda wasu suka dinga kone tayoyi da fasa shagunan mutane.
Wannan ya haifar da takun-saka da jami’an ‘yansanda wadanda a kokarin tarwatsa masu zanga-zangar, suka harba barkonon tsohuwa tare da yin harbi a iska.
Wani shaida da ta bayyana sunata a matsayin Ahmad, ya bayyana yadda zanga-zangar ta kasance.
“Ba a samu rahoton asarar rayuka ba ya zuwa yanzu. Bata garin da suka yi kone-kone, sun fito sun fara haddasa barna wanda ya sa ‘yansanda suka fara harbi,” in ji Ahmad.
Ya kara da cewa mazauna yankin sun taimaka wa ‘yansanda wajen korar bata garin, tare da tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.
Leadership ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun yi watsi da dokar hana fita da ke ci gaba da aiki kamar yadda gwamna Abba Yusuf ya bayar da umarnin domin dakile tashin hankali.
Ga hotunan masu zanga-zangar a kasa: