Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta karrama wasu jami’anta sakamakon bajinta da suka nuna wajen gudanar da aiki tuƙuru.
Hukumar NIS ta karrama jami’an ne a domin bikin ranar abokan hulɗa ta duniya ta 2022, da hukumar ta gudanar shalkwatarta da ke Abuja yau Juma’a, 7 ga watan Oktobar 2022.
Da yake jawabi yayin karramawar, shugaban hukumar ta NIS, CGI Isah Jere Idris ya bayyana cewa wannan babbar rana ce mai matuƙar muhimmanci ga hukumar ta NIS wajen gabatar da nasarori da ta cimma a lokacin gudanar da ayyukanta.
“Mun saba gudanar da murnar wannan rana wajen mayar da hankali kan abokan hulɗa wato mutanen da muke wa hidima. A duk lokacin da muka mayar da hankali wajen yi wa abokan hulɗa ayyukan da suka dace, to lallai za mu samu jinjina ta musamman daga gare su wanda zai ƙara mana zimmar yin aiki tuƙuru.
“Ya zama dole a wannan rana mu karrama wasu daga cikin jami’anmu waɗanda suka yi aiki tuƙuru duk da irin ƙalubale da muke fuskanta amma suka jajirce wajen gudanar da aiki yadda ya kamata. Mun ga ya kamata mu karrama su a daidai ranar da muke murnar abokan hulɗa ta duniya.
“Wannan rana ta kasance kusan watanni 8 da muka yi biki makamancin haka a NIS a watan Fabrairun 2022, ga shi ya sake faɗowa a daidai wannan lokaci mai albarka.
“Ina da ajandoji guda uku waɗanda suka haɗa da kyautata jin daɗin jami’ai, kula da iyakokin ƙasa da kuma inganta ayyukan bayar da fasfo.
“A kan abubuwan da suka shafi jin daɗin jami’ai wanda muke murna a wannan rana kuwa, mun yi ƙoƙarin buɗe asusu na musamman domin tallafa wa iyalan jami’anmu waɗanda suka mutu a bakin aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya. Haka kuma muna ƙoƙarin bai wa jami’anmu abubuwan da suke buƙata musamnman wajen biyan su haƙƙoƙinsu domin samun ingancin aiki.
“Tun lokacin da na karɓi ragamar shugabancin hukumar NIS, na gaji basussuka na biliyoyin nairori. Bayan na tattauna da mahukunta, mun miƙa ƙuduri ga gwamnati ta hanyar ma’aikatar da take kula da ayyukanmu domin ƙarin kuɗaɗe da zai ba mu damar biyan bashi. Ina fatan za mu samu nasarar amincewa da buƙatarmu.
“Mun kasance muna da tsarin karrama jami’anmu waɗanda suke aiki tuƙuru domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da aiki yadda ya dace. Wannan karramawa ta kasance yabo da jinjina ga jami’ai wajen ƙara jajircewar gudanar da aiki a hukumar NIS.
“A irin wannan biki da muka gudanar a watan Fabrairu, mun samu nasarar karrama jami’ai guda 30 bisa gudanar da aiki tuƙuru. Amma a wannan karon jami’ai 8 kaɗai muka karrama domin yaba musu kan gudummuwar da suka bayar na gudanar da aiki yadda ya kamata.”
Ya ƙara da cewa hukumar NIS tana alfahari da dukkan jami’anta wajen ƙoƙarin yi wa ‘Yan Nijeriya ayyukan da suke buƙata. Ya ce bisa ƙoƙarin jami’an ne ma ya sa sau uku bi-da-bi hukumar tana zama gwarzuwa da ta lashe kambi a tsakanin ma’aikatun gwamnati. Ya ce da wannan ne yake jinjina da dukkan jami’ai da suke zama silar nasarar da hukumar ke samu wajen zama ta ɗaya.
A cewarsa, hukumar ta NIS za ta ci gaba da zage damtse wajen gudanar da ayyukanta cikin tsari da ƙwarewa domin yi wa ‘yan Nijeriya ayyukan da suke buƙata ba tare da wata matsala ba.