Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya bayyana nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da wani gagarumin kokari da ke nuna hadin kai tsakanin yankunan Nijeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ranar Lahadi a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya ta bana da aka gudanar a fadar gwamnatin Jihar da ke Birnin Kebbi.
- 12 Ga Yuni Sam Ba Ta Dace Da Ranar Dimokradiyya Ba A Nijeriya —Ra’ayin Najib Sani
- 12 Ga Yuni: Atiku, Tinubu Da Obi Da Ragowar Wasu Za Su Sanya Furanni A Kabarin Abiola
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, wanda shi ne shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron zaben jam’iyyar APC na kasa.
,Bagudu wanda shi ne, shugaban kungiyar gwamnonin APC na Nijeriya ya ce, ” Dan takarar ya samu kuri’u a fadin kasar nan ba tare da la’akari da kabilanci da Addini ko yanki ba.” Cewar Bagudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp