ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

12 Ga Yuni Sam Ba Ta Dace Da Ranar Dimokradiyya Ba A Nijeriya —Ra’ayin Najib Sani

by Leadership Hausa
4 years ago
12

Tun shekarar 2018 lokacin da ke yakin neman tazarce ya aiyana 12 ga watan Juni na ko wace shekara a matsayin ranar dimokradiyyah a maimakon 29 ga watan mayu.

Hakika shugaban kasa yana da hurumin ware ko wace rana a matsayin ranar hutu a kasa.

  • 12 Ga Yuni: Muhimman Abubuwan Da Buhari Ya Fada A Jawabinsa Na Ranar Dimokuradiyya
  • 12 Ga Yuni: Atiku, Tinubu Da Obi Da Ragowar Wasu Za Su Sanya Furanni A Kabarin Abiola

Sai dai kuma a tunani na, 12 Yuni ba ita ce tafi dacewa da ranar dimokradiyya ba saboda ba wata hujja mai karfi da zai sa 12 ga Satan Yuni ta zamo ranar tunawa da dimokradiyyah a Nijeriya saboda dalilai masu zuwa da zan bayyana.

ADVERTISEMENT

A gani na, 29, ga watan mayu, ita tafi dacewa fiye da kowace ranar a matsayin ranar dimokradiyya. Da farko idan muka dubi tarihin zabukan Nijeriya daga 1923 zuwa yau, zamu ga cewa zaben 1999 zuwa yau shi aka fi samun nasara.

Misali, zaben 1923 wanda shi ne na farko a Nijeriya bai ba wa ‘yan kasa cikakken dama ba, saboda yan majalisu ne kawai aka ba wa ‘yan kasa damar zaba yayin da masu mulkin mallaka suke shugabancin gwamnatin tarayya.

LABARAI MASU NASABA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

Sa’annan kuma yan shekara 21 zuwa sama wadanda suke iya mallakar kudi a kalla £100 a shekarar data gaba ci zabe su ne kadai aka basu damar kada kuri’a.

Kazalika, wadanda aka yanke musu hukuncin kisa, ko zaman kurkuku na fiye da shekara guda, ko masu tabin hankali duk an haramta musu zabe a lokacin.

Su kansu ‘yan majalisun da aka zaba, shugaban mulkin mallaka na lokacin Clifford ya nada mutane 13 cikin yan majalisu a matsayin ‘yan majalisa baya ga zababbun.

Daga cikinsu akwai wakilan’ yan kasuwa da jami’an banki, masu tonan ma’adanai da masu jiragen ruwa.

Ya nada wasu kuma su wakilci jihohi da ake cewa cibiyoyin kasuwanci ne kamar su Kalabar da Kano da Legas da Fatakwal.

Zaben da aka sake yi bayan wancan shi ne na 1959 lokacin samun ‘yancin kasa wanda ake cewa jamhuriya ta farko. An yi zaben ranar 12 ga Disamba 1959, Sai dai an samu juyin mulki daga sojoji shekara shida kacal bayan kafa gwamnatin farar hula kuma ba a sake zabe ba sai 1979 lokacin da Shagari ya kayar da Awolowo.

Duk zabubbukan jumhuriya ta farko da ta biyu zabuka ne da aka gudanar bisa kabilanci. Jam’iyyun lokacin suma duk suna wakiltar bangarori ne ma’ana sashi-sashi a madadin su zamo Jam’iyyun kasa. Don haka suma jumhuriya na farko da ta biyu basu chanchanci zama ranar tunawa da dimokradiyyah ba.

Ranar 6 ga watan Augusta 1983, an sake yin zabe yadda Shagari ya zarce amma bai dade ba janar Muhammadu Buhari ya masa juyin mulki.

Tun daga lokacin sojoji ne suke ta mulkar Nijeriya har shekarar 1993 lokacin da janar Ibrahim Babangida ya yanke shawarar mika mulki ga farar hula bayan ya fahimci tsarin dimokradiyyah yana ci gaba da samun karbuwa a mafi yawan kasashen duniya.

Shi wannan zaben an gudanar dashi ne ranar 12 ga watan Yuni tsakanin Moshood Abiola da Bashir Tofa. Abiola shi ne ake ikrarin ya lashe zaben inda ya samu kuri’u miliyan takwas da doriya yayin da Bashir Tofa, ya samu kuri’u miliyan biyar da doriya. Saidai kafin a sanar da wanda ya lashe zaben, Babangida ya soke zaben bisa wasu dalilai na shi.

Al’amarin ya janyo cecekuce da zanga zanga musamman a garuruwan yarbawa. Da yaji wuta sosai Babangida daga baya ya nada Shonekam daga yankin da Abiola ya fito don kwantar da hankalin kasa. Amma duk da mika mulki da Babangida ya yi wa Yarbawa lokacin bai sa ya yi farin jini a gun ‘yan uwanmu yarbawa ba, don har yanzu suna sukarsa don soke zabe mai inganci.

Kash! Kafin gwamnatin riko da Babangida ya nada don ta sake shirya sabon zabe, sai ga janar Sani Abacha ya zo ya kifar da gwamnatin kuma ya yi ta mulki har 1998 lokacin da wasu da har yau ba a san su waye ba suka kashe shi.

Daga nan ne dimokradiyya ta samu damar da bata taba samu ba a Nijeriya bayan janar Abdulsalam Abubakar da ya maye gurbin Abacha da shirya ingantaccen zabe da ya kawo Olusegun Obasanjo a matsayin sabon shugaban farar hula bayan ya kayar da Olu Falae.

Tun lokacin da dimokradiyyah ta samu gindin zama a kasar nan yau shekara 23 a jere ba tare da sojoji sunyi juyin mulki ba. An rantsar da shi ne ranar 29 ga mayu 1999 tare da gwamnoni 36.

Bisa wadannan dalilai nake cewa ranar 29, ga mayu ita tafi chanchanta ta zama ranar da ringa tunawa a matsayin ranar dimokradiyyh a maimakon 12 ga watan Yuni a Nijeriya.

Karin hujjojin sune; sabanin zabukan 1959, 1979, 1993 da aka soke ko aka gudanar bisa turbar kabilanci da bangaranci da rikice rikice ko kuma juyin mulki daga sojoji, zaben 1999 ya fi nuna hadin kai tsakanin ‘yan Nijeriya.

Alal misali, Obasanjo ya yi takara da dan uwansa Bayerabe kuma wanda suka fito daga yanki daya wato, Olu Falae saboda Obasanjo dan jihar Ogun ne shi kuwa Falae daga Ondo yake.

Abu na gaba, Obasanjo bai bawa yan Nijeriya kunya ba lokacin mulkinsa domin ya yi kokari wajen daura kasar a turbar ci gaba, ya kuma samar da tsaro da hada kan ‘yan Nijeriya da kafa hukumomin yaki da rashawa.

Kazalika, zaben 12, ga Yuni na shekarar 1993 ba shi ne na farko ba a Nijeriya, ba shi bane wanda yafi ko wanne zaman lafiya ba, ba shi bane kuma wanda ya daure ba, to ta yaya ta zamo ranar dimokradiyya a Nijeriya?

Maganar da nake yi shi ne 29, ga Satan Mayu ita tafi dacewa da ranar dimokradiyya tunda ita ce ta daure a matsayin ranar da farar hula suka mika mulki ga farar hula shekara 23 yanzu.

12
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki
Bakon Marubuci

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara
Bakon Marubuci

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
Bakon Marubuci

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

June 5, 2026
Next Post
Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Gabatar Wa Amurka Bukatar Sin A Fannoni 4

Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Gabatar Wa Amurka Bukatar Sin A Fannoni 4

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.