ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tun Ina Yaro Harkar Fim Ke Birge Ni —Abba Harara

by Sulaiman
4 years ago
Abba Harara

Daya daga cikin Shahararrun Marubutan fina-finan Hausa, kana matashi mai shiryawa wanda ya shafe shekaru goma cikin masana’antar Kannywood wato ABBA ABUBAKAR MUHAMMAD Wanda aka fi sani da ABBA HARARA ya bayyana dalilinsa na maida hankali ga shirya fin nasa na kansa, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim. Ga dai tattaunawar tare da Wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Ya sunan Malamin?
Sunana Abba Abubakar Muhammad amma an fi sanina da Abba Harara.

Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Toh an haifeni A Garin Kano Unguwar Gama ‘Brigade’ nayi ‘Primary’ da ‘Secondry’ A Suntulma Dake Unguwar Gama, na tsaya iya ‘Secondry’ ban ci gaba ba sai kuma Allah ya kawo ni masana’antar Kannywood.

ADVERTISEMENT

Cikin sunanka na ji an hada da Harara, A ina ka samo sunan Abbah Harara?
Na samu sunan a wajen Aisha Aliyu Tsamiya, ba na mantawa ita ce ta saka min kuma cikin ikon Allah ya bini.

Wanne rawa kake takawa a cikin masana’antar Kannywood?
Ina taka rawa guda 2 a cikin masana’antar Kannywood. Na 1 ni Marubuci ne, na 2 kuma ni mai shiryawa ne wato ‘Producer’.

LABARAI MASU NASABA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Tun ina yaro harkar fim take birge ni kwarai da gaske.

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Abin dai kam sai godiya duk da gaskiya ni ban sha wuya wajen shiga ba.

Za ka yi kamar shekara nawa cikin masana’antar?
Zan yi kamar shekara 10.

Ga ka marubuci kuma mai shiryawa, toh tun a farkon da ka fara rubutun kana shirya fim ne ko kuwa iya rubutun kake daga baya kuma ka dora da shiryawa?
Tun farko ni marubuci ne ban taba tunanin ma zan kasance daga cikin masu shirya fina-finai ba, Amma cikin ikon Allah sai na samu kaina a wannan bangaren.

Taya za ka yi wa masu karatu bayanin yadda aka yi har ka fara shirya fim?
Akwai lokacin da za ki ga wasu daga cikin mutanenmu basa daukar labarinka yadda ka tsara shi to wannan yana kashe martabar labari shi ne kawai abin da ya bani kwarin gwiwar nima na soma shirya nawa da kaina.

Farkon da za ka fara shirya fim naka na kanka shin ka nemi taimakon wani ko kuwa kai tsaye ka fara?
A’a! Ban nemi taimakon kowa ba.

Ko akwai wani dan kalubale da ka fuskanta a lokacin, ganin cewar shi ne farkon farawar ka, musamman yadda za ka harhado kan su Jaruman da kake son su taka rawa cikin fim din?
Toh! kin san ba a rasa matsala a yayin farkon somawa amma Alhamdulillah gaskiya sai godiya kawai.

Mu koma batun rubutu, lokacin da za ka fara ka nemi taimakon wani ne ko kuwa da kanka ka zauna ka fara rubutawa?
Gaskiya akwai wanda ya shige min gaba a harkar rubutu shi ne ma ya koya min yadda ake rubutun labarin fim ba na taba mantawa, Sunanshi Sani Ata.

Wanne fim ka fara rubutawa kuma wanne ka fara shiryawa ?
Fim din da na soma rubutawa shi ne Ranar Suna, wanda na soma shiryawa kuma shi ne Malamin Kauna.

Kamar wadanne Jarumai ne suka fito cikin fim din?
Ali Rabi u Ali Daddy da Aisha Aliyu Tsamiya da Tanimu Akawu da Isyaku Jalingo.

Nawa ne adadin fina-finan da ka rubuta da kuma wanda ka shirya?
Wanda na rubuta ba za su wuce 50 ba wanda kuma na shirya ba za su wuce 5 ba.

Wanne abu ne ya fara baka wahala lokacin da za ka fara rubutu da kuma lokacin da ka fara kokarin shirya fim da kanka?
Toh gaskiya lokacin da zan rubutu na kan kwana na wuni ban iya rubuta komai ba saboda duk abin da ya kasance nazari ne to yana bukatar dogon tunani. Haka da na soma kokarin shirya fim na kaina na sha wahala saboda abu ne wanda ba ka taba yi ba sai kuma ka zo za ka yi to za ka fuskanci abubuwa da dama.

Toh ya batun dawowar kudaden da aka kashe, musamman bangaren shirya fim din?
A gaskiya kudi basa dawo wa a harkar fim kawai muna yi ne saboda sabo kuma kawa zuci saboda harkar fim tana da shiga rai.

Kamar yanzu da fim ya koma kan ‘You tube’ ake Siris fim ya kuke iya fidda kudadenku har kuke biyan sauran Jaruman da za su fito cikin fim din, ko kuwa yanzu ba biya ake yi ba kawai ana yi ne ya fi ba a yi ko kuwa?
Dole za ka biya Jarumi sannan idan ‘YouTube’ din ka ya kai wani mataki za a soma biyanka duk da hakan baya dawo da kudin da ka kashe sai dai ka dan samu abin da ka samu kawai.

Kamar shi rubutun fim din, idan kuka rubuta siyar wa kuke yi ga masu shiryawa, ko kuwa kyauta kuke bayar wa ganin ku ne marubutan duk kuna tare?
Siyar wa muke yi ko kuma furodusa ya ce ka yi masa rubutu ya biya ka ba kyauta bane.

A cikin naka rubutun fim din wanne ne ka siyar da shi da tsoka wanda ba za ka taba mantawa ba
Akwai wani sunansa ATM.

Ko za ka iya fado wa masu karatu sunayen fina-finan da ka rubuta ko da kadan ne?
Akwai Fauwaz, Farida Nabil, Sirrin Zuciya, Bani da laifi, Makullin Zuciya, Maraicin ‘Ya Mace, Ruhin Mijina, Sadeek Sanam, da dai sauransu.

Za mu ci gaba mako me zuwa

Abba Harara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

June 14, 2026
Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Next Post
Zargin Tayar Da Tarzoma: An Damke Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Kogi

Zargin Tayar Da Tarzoma: An Damke Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Kogi

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.