Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da sauye-sauye a bangaren da ya shafi ma’aikatan gwamnati kai tsaye, tsarin fansho, da kuma tsarin samar da ayyukan yi, a wani mataki na sake fasalin harkokin mulki da inganta ayyukan gwamnati a jihar.
Da yake jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a Kano, Gwamna Yusuf ya sanar da sake inganta dokokin da suka shafi Ma’aikatan Gwamnati, Ka’idojin Kudi, da Tsarin Ma’aikata.
- Hukumar Shari’a Ta Dakatar Da Magatakarda 2, Ta Kuma Gargaɗi Alƙalai 2 A Kano
- ‘Yan Siyasa Na Komawa APC Don Buƙatar Kansu, Ba Don Jama’a Ba – Dalung
“Manufarmu ita ce, samar da ƙwararrun ma’aikatan gwamnati na zamani, wadanda za a ga ƙwazonsu a fagen aiki,” in ji Yusuf.
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho.
A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar.
Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu.
Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000 ga ma’aikatan jihar domin dakile wahalhalun da ma’aikatan jihar ke ciki da kuma bunkasa ayyukan noma a jihar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp