Ranar 5 ga watan Oktoba na kowace shekara ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin bikin ranar malamai ta duniya.
An ware ranar don nuna girmamawa da kuma karrama su kan irin namijin kokarin da suke yi wajen ilimantarwa da kuma bai wa yara tarbiyya.
- Mahakar Danyen Mai Ta Daqing Ta Samar Da Tan Biliyan 2.4
- Atiku Ya Karbi Mutane Dubu 25 Da Suka Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP A Bauchi
Taken bikin ranar na wannan shekarar shi ne: Mafita da hanyoyin inganta rayuwar malamai.
Sai dai a wannan lokaci Leadership Hausa, ta cikin shirin ‘Twitter Space’ da yi, ta zanta da wasu masana kan yadda aikin malamanta yake a da, da kuma yanzu.
Sannan kai tsaye a cikin shirin na kafar Twitter sauran jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu kan yadda aikin yake da kuma irin hobbasa da suke ganin malamai na bukata da ma shi kansa ilimin.
Daya daga cikin wadanda suka tsinkayin shirin, mai suna El-Faruk, ya ce akwai bukatar yi wa malamai adashin gata don samun nutsuwar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
“Malami yana da abubuwa da dama da za su taimaka masa don bunkasa ilimi. Ma’ana dole ne gwamnati ta inganta aikin malamai da kula yanayin kula da su.
“Sannan a matsayinmu na dalibai yana da kyau muke waiwayar malamanmu walau na Firamare, Sakandare ko kuma na tsangaya, saboda da yawan irin wadannan malamai na fama da yanayin rayuwa saboda halin rayuwa da kasar nan ta tsinci kanta a ciki.
“Mu kyautata musu ko mu dauki karatun wasu daga cikin ‘ya’yansu,” a cewar El-Faruk.
Shi kuwa Abdul Rahman, cewa ya yi akwai bukatar iyaye da dalibai su san darajar malamai.
“Iyaye da dalibai ya kamata su san darajar malamai, saboda wasu sha’awa ga aikin ce tasa suke yi, sai dai wasu na musu kallon kaskanci wanda hakan ya sa ake yi wa fagen kallon hadarin-kaji.”
Wani abu daga cikin hanyoyin walwala da aka yi wa malamai shi ne, kara wa’adin ritaya na malaman, wato daga shekara 60 zuwa 65, sannan gwamnatin tarayya ta yi alkawarin ingata wasu abubuwa da suka shafi albashi da alawus-alawus nasu.
Kazalika, an kalli irin badakalar da ake tafkawa a bangaren aikin malamanta wanda suka lalata da dalibai musamman mata a wasu lokutan ma har da maza, lalata don neman maki.
Wasu sun ce duk da cewar akwai malaman da ake samu da irin wadannan laifuka, amma wani kaulin daliban matan ne ke kai kan su don yin lalata da su don cimma bukatarsu musamman wajen ganin sun ci jarabawa da sauransu.
Amma wasu na ganin gudunmawar da suke bayarwa, ita ce abin da ya kamata jama’a su fi mayar da hankali, saboda girman abin da suke yi ya fi karfin auna shi a ma’auni.
Amma, gwamnati ta tanadi hukunci ga baragurbin malamai da aka samu da irin wannan laifi.
Matsalolin da ke tattare da harkar ilimi a Nijeriya na da tarin yawa, akwai karancin malamai, karancin walwalar malamai, cunkoson dalibai a azuzuwa, karancin albashi da sauran tarin matsaloli.
Mutane da dama sun bada gudunmawa ta hanyar kira ga gwamnatoci daga kowane mataki da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da su taimaki harkar ilimi don samar da manyan gobe masu hikima, da za su saita wannan kasa a nan gaba.