Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatoci daga dukkan matakai da su taimaka wajen bunkasa ilimi a kasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana haka ne a lokacin bikin ranar Malamai ta Duniya da ake gudanarwa a kowace ranar 5 ga watan Oktoba.
- Adadin Hada-hadar Kudaden RMB Tsakanin Sin Da Kasashen Dake Cikin Shawarar BRI Ya Karu A shekarar 2021
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Abuja-KadunaÂ
Atiku, wanda ya yi wajabi a lokaci bude cibiyar S.H.E a Abuja, a ranar Laraba, ya ce abun takaici ne ganin yadda ilimi ke samun koma baya daga wajen wadanda alhakin kula da shi ke kansu.
S.H.E wata kungiya ce da matar Atiku, Hajiya Titi Amina Abubakar ta bude don kula da yara kananan masu fama da cutar kwakwalwa.
A cewar Atiku, rashin kulawa da fagen ilimi ke samu shi ne ya haddasa wa malaman Jami’o’i tsunduma yajin aiki sannan ya kawo tsaiko ga ilimi.
Atiku ya ce “Duba da yadda talauci ke karuwa a tsakanin mutane, hanya mafi dacewa, ita ce a yi wa ilimi tagomashi. Idan mutane suka samu ilimi hakan zai taimaka musu wajen samar da arziki da rayuwa mai kyau ga iyalansu da kuma al’umma.
“Da yawan matsalolin da muke fuskanta a yau na da alaka da rashin ilimi da talauci da ya yi wa mutane katutu.”
Da take jawabi a wajen taron, matar Atiku, Hajiya Titi Abubakar, ta ce kungiyar an kafa ta ne don warware damuwar da mutane ke ciki a yanzu.