Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya kara jaddada aniyar Hukumar domin kara daga ‘yancin mata da ke aiki a Hukumar da kuma kaucewa nunawa masu dukkan wani na’ui na wariyar jinsi.
Dantsoho ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar mata ta duniya na 2025, inda ya jaddada cewa, Hukumar ta NPA ta mayar da hankali wajen samar da damarmaki don tallafawa mata da ‘ya’ya mata, domin su cimma burinsu, da suka sanya a gaba.
- NPA Za Ta Yunkuro Don Zamanantar Da Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya – Dantsoho
- Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
Ya kara da cewa, Hukumar na ci gaba da samar da shirye-shiryen da za su tallafawa mata, musamman wajen mayar da hankali kan wanzar da tsare-tsaren da za su bunkasa tattalin arzikinsu.
Dantsoho ya kuma zayyanao matakai iri-iri da Hukumar ta NPA ta kirkiro da su, musamman domin kara daga darajar mata, wadanda suka hada da, bai wa mata ma’aikatan Hukumar da suka samu juna biyu, tafiya yin hutun haihwa na wata shida.
Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, Hukumar na bai wa mata ma’aikatan Hukumar da ke shayar da jaransu damar tashi daga gun aiki da wuri, sabanin lokacin tashi daga aikin.
Ya sanar da cewa, yanzu a Hukumar ana kara samun nada mata kan madafun iko, inda ya sanar da cewa, a yanzu a Hukumar mace ce, ke rike da mukamin Babbar Darakta ta sashen kudi da mulki wato uwargida Bibian C. Richard-Edet.
A cewarsa, a shekarun baya, akalla muna da mata sha biyu da suke rike da mukamain Janar Manaja da kuma mukamain Manajoji a Hukumar
Shugaban ya bayyana cewa, mata na ci gaba da bayar da gudunmawar su wajen habaka fannonin da ke a Hukumar ciki har da bangaren tsaro, kiwon lafiya da sauransu.
“Wadannan wasu misalai ne ‘yan kadan da Hukumar ke yi na inganta ‘yancin mata da tabbatar da ‘yancin su, duba da cewa, bamu iyakance irin kokarin da mata suke da shi ba,” A cewar Dantsoho.
Duk da samar da wadannan ci gaban a Hukumar Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar za ta ci gaba da sauye-sauyen da za su gaba da kare ‘yancin matan da ke aiki a Hukumar.
Kazalika, Dantsoho Hukumar ta NPA za ta ci gaba goyon bayan kare ‘yancin matan da ke aiki a Hukumar da kuma tallafa masu.
“A matsayin mu na Hukumar mun yi alkawarin ba za mu yi kasa a guiwa wajen goyon bayan ‘yancin mata da kuma ‘ya’ya mata da ke aiki a Hukumar, da kuma sauran matan da ba a Hukumar suke yin aiki ba,” Inji Dantsoho.
Dantso ya kuma taya matan da ke aiki a Hukumar murnar zagoyowar ranar ta mata ta duniya, inda ya ba su tabbacin cewa, Hukumar za ta ci gaba da zama a kan gaba wajen samar da damarmaki ga da ‘yan mata da ke a fannin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp