A ci gaba da gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga al’ummar kasar nan a ranar Asabar 1 ga Oktoba, 2022 da misalin karfe 7 na safe.
An umarci gidajen talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da ayyukan gidan talabijin na Nijeriya (NTA) da Rediyon Nijeriya don yada shirye-shiryen.
- 2023: Sarkin Kano Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sahihin Zabe
- Bana An Noma Masara Da Tsadar Gaske – Makarfi
An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Femi Adesina, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, ranar Juma’a.
Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa ranar 1 ga Oktoba, 2022, za ta kasance ranar jawabin bikin mulkin Buhari na karshe ga Nijeriya a matsayin shugaban kasar.
A karshe Buhari zai kammala wa’adinsa na shugaban kasar Nijeriya na tsawon shekaru takwas a 2023.