Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya ce, gwamnatinsa za ta kafa gidauniyar tattara kudade domin biyan bukatun iyalan jaruman da suka rasu a bakin aiki.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bikin ranar tunawa da sojojin Nijeriya na shekarar 2024 da aka yi ranar Litinin a Kano.
- Gwamnan Abba Gida-gida Ya Rushe Duk Nade-nade, Ya Kwace Duk Kadarorin Gwamnati Da Ganduje Ya Sayar
- Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Bayan An Farmake Su Bisa Zargin Sakaci Da Aiki A Ekiti
Ya ce, gwamnatinsa za ta gayyaci manyan mutane a jihar domin su mara wa gwamnati baya wajen kafa gidauniyar tallafawan.
A cewarsa, za kuma a yi amfani da gidauniyar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da samar da ayyukan yi ga matasa.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa, Jiharmu ta dore da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma gwamnatinmu ba za ta bar komai a baya ba don aiwatar da wannan kyakkyawar aniyar,” in ji shi.
Da yake jawabi kan iyalan jaruman sojojin da suka rasu, gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen kyautata rayuwarsu.
Ya kuma bayyana cewa, iyalan jaruman da suka rasu, za su ci gajiyar tallafin da za a raba wa al’ummar jihar.
Gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.