Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin yaran Nijeriya sun cimma burinsu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar yara ta 2024 ta duniya, inda ya kara da cewa, yaran Nijeriya, su ke dauke da ragamar ci gaban Nijeriya.
- Malaman Kano Sun Roki Tinubu Ya Bari A Yi Sulhu Kan Rikicin Masarautar Jihar
- Gwamnoni 9 Da Har Yanzu Ba Su Babe Da Iyayen Gidansu Ba
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban ya ta ya iyaye, da wakilan iyaye murnar ranar a fadin kasar.
Ya yi kira da a mutunta iyaye a matsayinsu na makarantar farko ga yara da suke bayar da tarbiyya don kasancewarsa yara zama shugabanni na gari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp