Dakarun sojojin Ukraine sun janye daga birnin Lysychansk da ke da muhimmaci ga kasar, bayan da Rasha ta ci gaba da samun nasara wajen kwace ikon yankin gabashin Lugansk.
A farko dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya musanta ikirarin Moscow na cewa sojojin ta sun kwace ikon birnin, inda ya yi gargadin cewa yankin da birnin ya ke zai iya komawa hannun Rasha.
- Girgizar Kasa Ta Hallaka Mutane 42 A Indiya
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Hana Hakar Ma’adanai
Dama dai Rasha ta yi ikirarin kwace birnin, wanda hakan ke da muhimmanci ga dakarun na Moscow da ke nema kwace iko da gabashin Ukraine, fiye da watanni hudu da mamayar da suka yi, bayan sun karkata akalarsu daga babban birnin kasar Kyiv.
Magajin garin Sloviansk, mai tazarar kilomita 75 daga yammacin Lysychansk, ya ba da rahoton harin da Rasha ta kai da cewar, mutane shida sun mutu ciki har da wani yaro, yayin da wasu 15 suka jikkata hadi da tashin gobara daban-daban.
Rasha ta zargi Ukraine da harba makami mai linzami guda uku kan birnin Belgorod da ke kusa da iyakar Ukraine a yammacin Asabar, inda Belarus ta ce ta kama makamai masu linzami na Ukraine.
Lysychansk ya kasance babban birni na karshe a yankin Lugansk na Donbas da ke hannun Ukraine kuma kama shi na nuni da kara matsawa a yankin gabashin da Rasha ta yi.