Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana damuwarsa kan yadda matasa ke tashe-tashen hankula sakamakon rashin aikin yi.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Financial Times a ranar Talata.
- Tuni Tallafin Man Fetur Ya Dawo – Obasanjo
- Gwamnatin Nasarawa Ta Amince Da Biyan 70,000 Mafi Karancin Albashi
“Matasanmu suna cikin tashin hankali. Kuma suna cikin tashin hankali ne saboda ba su da fasaha. Ba su da karfi. Ba su da aikin yi.
“Dukkanmu muna zaune a kan wani abu da zai iya fashewa. Kuma addu’ata ita ce mu yi abin da ya dace kafin lokaci ya kure,” in ji shi.
Kalaman na Obasanjo na zuwa yayin da ake zanga-zangar #Endbadgovnance da ke gudana a duk fadin kasar da matasa suka yi kan yunwa da kuncin rayuwa a kasar.
Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne dai matasa a fadin kasar suka fara zanga-zangar.
Da yake karin haske, Obasanjo, ya ce da tattalin arzikin Nijeriya zai yi kyau matuka idan ba a dogara ga samar da danyen mai kawai ba.
Ya bayyana dogaro da danyen man da kasar ke yi a matsayin “mummunan kuskure”.
“Na yi imani mun tafka babban kuskure ta hanyar sanya kwayayenmu duka a cikin kwando daya ta hanyar dogaro da mai. Muna da kaya masu muhimmanci, iskar gas, amma ba ma duba su,” in ji shi.
Akwai kuma gazawar Kamfanin Man Fetur Kasa (NNPCL), Kamfanonin Mai na duniya, da sauran kamfanonin mai na kasa wajen inganta hako mai domin biyan bukatun kasar.
Obasanjo ya ce Nijeriya za ta iya zuba jari sosai a harkar noma mai makon kawai danyen mai.
“Amma mun yi watsi da harkar noma wacce za ta iya iya zama jigon jarinmu.”