Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira. Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, kama daga fannin zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da irin kalubalen da mafi yawan ‘Yan Mata ke fuskanta wajen samarinsu, har ma da matan aure gaba daya, na game da rashin ba su kulawa da samarinsu ko mazajensu ke yi, fiye da yadda suke bawa kallon kwallo ko buga kwallon, musamman a yayin kallon kwallon kofin duniya, inda hakan ke ci wa ‘Yan Mata tuwo a kwarya, sabida rashin basu kulawar da ta kamata.
- Muna Ci Gaba Da Kokarin Ceto Sojar Da Aka Sace – Sojoji
- Kotu Ta Sake Hana DSS Cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
A cewar wasu ‘Yan Matan samarin na kin daga wayarsu a duk lokacin da suke bukatar kiransu, sabida kallon kwallo ko buga kwallon.
Baya ga haka da rashin zuwa wajen ‘Yan Matan zance ko catin da dai sauransu. Sai dai ‘Yan Matan na ganin cewa; Ko kallon kwallon ya fi bawa ‘Yan Mata kulawa?, Wadanne hanyoyi samari ya kamata su rinka bi dan bawa ‘Yan Matansu kulawa?. Dalilin hakan wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka bayyana na su ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Hussy Saniey daga Jihar Katsina:
Gaskiya ‘yan mata da matan aure suna fuskantar kalubale mai tarin yawa a wajen maza a duk lokacin da aka ce za a buga irin wannan ball din, saboda a wannan lokacin ba su damu da damuwar kowa ba. Tabbas! a duk ranar kallon ball samari na nuna wannan ball din tafi ‘yan matansu. Saurayina yana kallon ball, kuma yana bugawa, don haka duk ranar da ake ball ko keyar shi ban gani har sai ya fito daga kallon. Idan kuwa aka yi rashin sa’a su aka ci wannan daren gaba daya ma ko waya ba mu yi, har sai lokacin da ya huce. Kamar yadda suke ba da kulawa ranar da ba a kwallo ya kamata ma ko da ana yi su bada irin wannan kulawar. Ya kamata su rinka ba wa budurwarsu kulawa fiye da ball saboda fifita ball da suke yi yana ci mana tuwo a kwarya.
Sunana Fatima Jafar Abbas daga Garin Rimin Gado:
Rashin kulawa a soyayya yana da tasiri wajen hana soyayya ta yadu, don soyayya tana yaduwa ne ta hanyar kulawa. Ya kamata su samari su zama masu kulawa gudun ka da soyayyarsu ta ruguje. A’a kallon ball baya gaba da kulawar da samari za su bawa ‘yan matansu kulawa ita ce gaba. saurayina yana kallo, sai dai baya bugawa, yana bani kulawa ne ta hanyar yawan kirana a waya da zuwa gidanmu don ya ga yaya nake. Ya kan ware lokacin kallon ball daban lokaci kulawa dani daban. Hanyoyin da za su bi; su rinka yawan kiran ‘yan matansu da zuwa gare su a lokacin da ba na ball tunda ba, 24hrs ake yi ana kallon ba ko buga wa. su rage yawan kallon ball da bugawa don hakan ya kan cinye musu lokaci har hakan ya janyo rashin kulawarsu ga ‘yan matansu.
Sunana Muhammad Kabir Kamji daga Batsari, Katsina:
Abin da za a ga ne da samari masu zuwa kallon ball shi ne; Samari sun dauuki kwallo da mahimmanci fiye da ‘Yan matansu, sabida wani saurayin kafin ya fara soyayya da ita wadda yake so din, yake yin ball, ko kuma kallonta. Kuma ya saba ba ta mahimmanci shiyasa ‘Yan matan suke ganin kamar ya fi daukar ball da mahimmanci bisa ga su. Ko kusa kallon ball baya kawo gaba, sai dai ma ya sa kayi abokai wurare-wurare, sannan ya danganta ga yadda ka dauki ball din amman ball ba ta haddasa gaba. Tabbas! ina yin ball kuma ina kallon ta sosai. hanyar da nake ba wa wadda nake so kulawa ita ce; Idan zan je ball zan ce da ita ball zan tafi kafin ‘time’ din bal din yayi, idan kallo ball din dan tafi zan sanar da ita ga inda zan tafi ko da ta kira bana kusa. Sannan ban hada bal da mosiyata ba ko wane da gurin sa, amman ina son ball sosai. Shawarata anan ita ce; su ci gaba da yadda suke lokaci ne, Suma matan ba kulawar za su basu ba, sannan mace idan ta ga ka damu da ita sosai akwai raini. Ina kira gare ku samari ku ci gaba da bawa ball mahimmanci ko ba komai motsa jiki ne, kuma motsa jiki abu ne mai amfani, sannan kallon ball za ka samu nishadin da ba lalle budurwar ka ta baka shi ba. ‘Ball is bery important but not more than girlfriend’.
Sunana Fauziyya S. Madaki daga Jihar Katsina:
Abun da zan ce shi ne; ya rage kallon ball din, sannan ya ci gaba da kulawa da ita, hakan zai kawo musu zaman lafiya, bai daina ball din ba kuma yana kulawa da ita yadda ya kamata. Kulawa da ‘yan mata shi ne; gaba da kallon ball, saboda budurwarka wani lokaci za ta zama matarka, da zarar kuma ta zama matarka kulawa da za ka bata lada za ka samu, shi kuma ball din sai dai yasa ka karar da lokacinka a banza, a karshema wanda ba ka so ya ci, sai ka ga ya ci, ka tashi da bacin rai da cizon yatsa. Saurayina yana kallon ball, yana bugawa amma ba sosai ba, kuma yana bani kulawa yadda ya kamata. Ni fa bana ganin laifin samari masu ball, tunda ball din ba kullum bane, ko da kullum ne kafin ya tafi kallon ball din ko kafin ya tafi bugawa, yana iya kiran sahibarsa ya ji lafiyar ta, so ni ban ga ta inda ball za ta haifar da matsala ga masoya ba, matukar sun zauna sun fahimci juna. Shawara ita ce; tun kafin lokaci ya kure musu su gyara, kafin sahibarsu ta samu madadinsu.
Sunana Mas’ud Sale Dokatawa:
A gaskiya samarin da ba sa bawa ‘yan matansu kulawa ba sa kyautawa, kallo ko buga ball daban, muhimmancin budurwa daban. kallon yana sa nishadi amma yana haifar da bacinrai, damuwa, gardama, bakin ciki, har ma ya kai ga yin fada a tsakanin masu kallo. Musamman ma ‘world cup’. Amma bawa budurwa kulawa yana tattare da farin ciki, nishawa, walwala, debe kewa da kasancewa cikin jin dadi. Sai dai suma ‘yan mata suna iya zamowa sanadiyyar damuwa, bacin rai da ban haushi. Kowanne saurayi da nasa ra’ayin.wani kallon ball ya fi bashi nishadi fiye da budurwa, wani kuma ba ya ma kallon Ball din gaba daya, ya fi bawa budurwa kulawa fiye da sauran abubuwan yau da kullum. Ni saurayi ne kuma bana kallon ball, amma ina bugawa kuma ba kullum ba, saboda ban dauke ta abin yi ba kawai don motsa jiki. Yin Ball ko kallonta baya hana ni bawa budurwata kulawa, saboda lokacin ball daban da lokacin bawa budurwa kulawa. Misali; Tn daga safe har karfe hudu na yamma (4:00pm) duk lokaci ne, da zan bawa budurwata da sauran abubuwan lokacin. Sannan na yi wasan ball karfe hudu zuwa shida (4-6) awa biyu kacal, ba za ta hana bawa budurwa lokaci ba. Hanyoyin da samari za su bi masu kallon ball ko bugawa wajen bawa ‘yan matansu kulawa sun hada da; Rage kallon Ball din, dan ba ta zana dole ba, musamman Ball din dare fahimtard a ‘yan matan hakan yana daga cikin abin da suke ra’ayi ne, don yi musu uzuri. Samari su gane cewa ball ba addini ba ce, amma bawa Dan Adam kulawa da kyautawa addini ne, akwai Lada. Rashin bawa mace kulawa na janyo rabuwa, batawa, ko rage tsakaninsu, musammanma wani saurayin yana ba ta kulawar da ka kasa bata. Shawarar ita ce; Rage kallon ball din ko ba za a daina gaba daya ba, su sani kallon ball bai da wata fa’idah, sai ma bata lokaci. samari su rika saba lokutan kallon ball din, da lokutan da za su bawa ‘yan matansu kulawa kamar zuwa hira, kiran waya, chatting, tedt sauransu. sanar da ‘yan matansu cewa; za su shiga wurin kallon, don su nuna musu cewa suna da muhimmanci a wajen samarin, hakan ma kulawa ce.
Sunana A. Ibrahim daga Jihar Kano:
Da farko dai shi ne; a gaskiya a ra’ayi na ba zai yu ace maza ba sa wa bawa matayan da suke so ko kuma in ce su ke kauna su ke da burin su auri junansu ba a ce ba sa ba su kulawa ba, sai dai kwai abin da zan iya cewa ‘majority’ matan ba sa kaunar kallon ball din, ko kuma buga ta. Shiyasa suke damuwa da haka. A’a! kallon ball baya gaba da kulawar da za ka bawa budurwarka wanda idan mai dika ya lamunce, yake so ta za matarka ko kuma in ce uwar yayanka. Eh! gaskiya duka ina yi amma kamar yadda ba kullum nake zuwa hira ba hakabma ba kullum nake kallon ball din ba, ko kuma in ce bugawa ba tinda ba kullum nake zuwa kallon ba da bugawa ba, tanan nake samin damar bata kulawa. Hanya ita ce kallon ball dai,-bai kai matarka mahimmaci ba ko kuma in ce bai kai wanda kake so za ka aura mahimmaci ba, kuma kyautatawa ga mata su dasu ja hankalin maza ga ni satar kallon ball din ku ko bugawa za ka ga wasu matar ba sa iya farantawa mazajan rai ,shiyasa wani ya fi bawa hakan mahimmaci. shawara ita ce yakamata dai idan kanayi kasami time da kuka warewa matanku karku mai da ita kamar abincinka kullum kullum baka da lokacin da daku bawa matanku kulawa.
Sunana Hajara Ja’afar daga Jihar Kaduna:
To agaskiya duk saurayin da bai baiwa macce kulawa, bai san ciwon kansa ba musamma ma wanda ya fi daukaka kallo akan iyalinsa, ya na gyara rayuwansa sosai. Ina kulawa da ‘yan mata ya fi komai, ba wai kallon ball ba, saboda kai da kanka kafi samu a duk sanda ka kasance tare da mace a duniya. a’a gaskiya ni saurayina yana buga ball kuma yana kallon amman dukkan wani kulawa da saurayi ke yi wa budurwa yana bani, sannan yana kallon ball din shi, amman kuma baya tauye min hakkina duk sanda ya kasance lokacin ball ne kuma ya kamata ya zo gurina, to baya zuwa sai dai in ya zo gurina ya gama hirarsa sannan in ya koma ya kalla bayan an gama. Hanya daya kamata abi shi ne; ya kamata su rika hakura in har lokacin kallon ya zo dai-dai da lokacin zuwa hira, ko kuma lokacin da iyali ke bukatar kulawarka to kayi hakuri daga baya ka kalla, tunda yana nan ba sai lalle ka kalla a lokacin da ake bugawa ba. Shawata ita ce; a gaskiya ya kamata dukkan wani saurayin da yake kallon ball ya kamata ya san time din da ya kamata ya kalli ball, ko kuma ya buga bal din don darajarka da kimarka, shi ne, ka bawa macce kulawa kai ma za ka samu kima fiye da wanda kake da shi bissalam.
Sunana Yakubu Obida daga Jihar Kano Unguwar Farawa:
Ba wai rashin kulawa ne Maza ba sa bawa Mata ba a lokacin da ake buga ball, musanman ‘world cup’ ba. Maganar gaskiya abubuwa an bar mu a baya sosai duk abin da dan uwanka yake so ya kamata kai ma ka san shi, wannan ba ma dan uwa bane abokin rayuwa ne ba a fatan wani abu ya raba har karshen rayuwa. So ya kamata ta daure ta koya tunda abun na ba su Nishadi in ba haka ba haka za ai ta rigima tunda ba abu ne marar kyau ba, balle a hana shi, sannan ya kamata ta rinka yi masa addu’a har ya zo ya daina. Gaskiya A’a hakan ba dai-dai bane. Eh! ina daya daga cikin masu kallon ball kuma ina buga ball hanyoyi na 1 da nake bi kafin in fita a lokacin da nake soyayya kenan zan fada mata zan ce zan je kallon ball kina da wani uzuri ne idan ta ce; ba matsala sai in tafi, Ni ba ma na zuwa kallon ball ‘online’ nake kallon ball kuma ina sanar da ita kar ta ganni ‘online’ ta dauka kyale ta nayi. Ya kamata kowane bangare ya fahimci abu me mahimmanci a zaman soyayya ko ma aure baki daya a tsaya a bawa juna kulawa, kuma shi me kallon ball ya sallami budurwar sa tukaunna kafin lokacin tafiya kallon ball. A gaskiya samari masu kallon ball kar ku fi bashi muhimmanci har ma abun ya zamar maka jiki ko akida ko kuma wani abu wanda in baka yi shi ba ba za ka ji dadi ba, ni na fi ba da shawarar ka sa data kai da masoyiyarka ko matar ka ku kalla tare ‘online’ saboda mahimmancinta a gurin ka.
Sunana Amina Abubakar daga Jihar Bauchi:
A gaskiya yana da kyau samari su dinga bawa ‘yan matansu kulawa, a ko wani lokaci saboda dan gibi kadan ne za ka bayar wajen mace yanzu ta samar maka madadi. Ba zan ce kallon ball yana gaba da kulawar mace ba, sai dai amma su ‘yan matan ne ya kamata su dinga yi wa maza uzuri ai ba ko yaushe ne ake kwana a gado ba, kuma dai kallon ball ai yanada lokaci, a gaskiya ‘yan mata mu dinga uzuri wa maza akan wannan. Tabbas! saurayi na yana kallon ball, a can baya ban son kallon ball, amma a yanzu dana hadu da mai son ball din wallahi ni kaina na koma kallon, so haka nan nake ta kallon shi mu yi ta hirar ball, ban mantawa lokacin ‘world cup’ din nan yana kallon kuma muna ‘communicating’ akan yadda ball din ke tafiya a WhatsApp, idan aka sha su in sha dariya idan mu aka sha ya sha dariya. Eh! yanada kyau su dinga tsakurar lokacina cikin na ball din, su dinga kulawa da ‘yan matan nasu saboda zaman lafiya. Daga karshe dai ina bawa ‘yan mata ‘yan uwana shawara, ku zama masu uzuri wa maza musamman akan ball, tunda a farko na fada shi ball din lokaci gare shi ba ko yaushe ne ake yin shi ba na gode.