• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Ilimin Iyaye Na Haifar Da Karuwar Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta (1)

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
Ilimi

Rashin ilimi tsakanin manya da matasa ya zama wata babbar matsala, wadda har ta sa masana suke ganin irin lamarin ne yake taimkawa wajen karuwar yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya.

Ilimin manya ana gane shi ne ta kason mutane daga shekara 15 wadanda suke iya karatu da rubutu, tare da fahimtar ‘yar karamar magana a kan rayuwarsu ta yau da kullum.

Gwamnatin tarayya ta kiyasta lamarin wadanda ke da ilimi ya kai kaso 69, wannan ya nuna ke nan kaso 31 har yanzu su  marasa ilimi, wanda kuma hakan yana nuna akwai mutane da yawa da basu da ilimi, wanda kuma hakan na nufin da akwai bukatar akwai abubuwan da suka kamata a yi ko daukar matakai dangane da hakan da zummar samun daidaiton da ake bukatar samu na wani mizani kamar fiye da kaso 90 na wadanda za su kasance masu ilimi.

  • Gwamnatin Tarayya Ita Kadai Ba Za Ta Iya Daukar Dawainiyar Kudaden Ilimi Ba – Minista
  • Gobara Ta Yi Sanadin Mutuwar Iyalan Kwamishinan Ilimi A Kano

Wadannan alkalumma da hukumar kula da kididdiga ta kasa ta fitar ya nuna sashen Arewacin Nijeriya shi ke da yawan al’ummar da basu da ilimi inda Jihar Yobe take mafi kankanta na kaso 7.23, Zamfara 19.16, Katsina na da kaso10.36 sai Sakkwato mai kaso 15.01, yayin da sashen Kudancin Nijeriya ke da yawan masu ilimi inda Jihar Imo ke jagorancin haka da kaso 96. 43, Legas kaso 96.3, Ekiti  kaso 95.79,sai Ribas da take da kaso 95.76.

Wannan kididdigar ta nuna da akwai wagegen gibi tsakanin sassan biyu wanda ya nuna da akwai bukatar a dauki mataki domin a cike shi gibin da ke da shi, na maganin matsalar da ta sa ake samun yara wadanda basu zuwa makaranta a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

A kokarin ta na cike gibin ko gurbin da ake da shi hukumar kula da Ilimin manya da yaki da jahilci a wani taron da ta kir ana masuruwa da tsaki a Abuja, na yadda za a cimma buri na karuwar masu ilimin da ake bukata.

Da yake jawabi lokacin taron mai taken” matsalolin da ake fuskanta na gano yawan yaran da basu zuwa makaranta da matasa babban sakataren hukumar,Farfesa.Simon Akpama,’ya ce taron na wadanda za su taimaka sun hada kansu ne domin domin bunkasa ilimin yaki da jahilci a Nijeriya.

Ya kara bayanin cewa ba wata maganar boye- boye lamarin rashin ilimi a tsakanin manya da matasa wata hanya ce da matsalar  yawan yaran da basu zuwa makaranta,ta biyo har ta samu wurin da zata boye.

“Bugu da kari  ya kara bayani duk kokarin da ake na ganin an gano bakin zaren,akwai matsalolin da suke samar da karan- tsaye a kokarin da ake na kawo karshen rashin ilimi ko yaki da jahilcin manya da matasa,hakan ke taimakawa wajen karuwar yaran da basu zuwa makaranta.

Ya kara jaddada cewa ganin yadda lamarin yake ne yasa aka ga yafi dacewa inda har aka dauki mataki na maganin ko kawo karshen babbar matsalar da take damun kasa, inda aka dauki matakin ganin  dukkan manya da matasa sun samu dama ta kasancewa masu ilimi bayan sun yaki jahilci.

Yayin da yake karin haske cewa ilimi bai tsaya kawa ikan iya karatu da rubutu ba,kamar yadda yace  “ ilimi wani tubali ne inda ake fara gina gaba, domin yana ba kowa damar bunkasa al’umma da cigaban  wajen samar da abubuwan more rayuwa”.

Babban sakataren yayin da yake bayani kan yadda za a fita daga matsalar kamar yadda yace lamarin yana hannun manya da matasa wadanda gabarasu ke da dama ta samar da ko kawo cigaba, “fatan da ake da ita da muradai ‘yan gida daya ne inda akwai hanyoyin karuwa masu dama in an samu yakar jahilci aka samu ilimi.”

Manufar wannan taron it ace kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su taimakawa kokarin da gwamnati take, inda iin aka hadza hannu daya za a iya gamawa da rashin ilimi ko jahilci, a sake saita ko daidaita tunanin manya da matasa su maida hankalinsu wajen bunkasa cigaban Nijeriya.

Akwai abubuwa da yawa wadanda suke taimakawa wajen karuwar jahilci a Nijeriya da suka hada da, jama’a kara yawa suke a Nijeriya, saboda karuwar da al’umma suke yi ne, shi yasa yawan wadanda basu yaki jahilci ba ke karuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Taron “Zurfafa Gyare-Gyaren Kasar Sin A Sabon Zamani Dama Ce Ga Duniya” Ya Kaddamar Da Jigo Da Zama Na Musamman Ga Kwararru

Taron “Zurfafa Gyare-Gyaren Kasar Sin A Sabon Zamani Dama Ce Ga Duniya” Ya Kaddamar Da Jigo Da Zama Na Musamman Ga Kwararru

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.