Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da harin da Boko Haram ta kai cikin makon nan a jihar Borno, inda ya bayyana shi a matsayin “kisan rashin imani” tare da kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci.
Harin, wanda ya auku a ranar Juma’a a ƙauyen Darajamal, da ke kan hanyar Bama zuwa Banki a dajin Sambisa, ya yi ajalin mutum 63, ciki har da Sojoji biyar da fararen hula 58, tare da ƙone gidaje da motocin jama’a, da sauran kayayyakin masu muhimmanci na ’yan gudun hijirar da aka mayar da su.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku, ya bayyana alhini kan kisan gillar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da wanda lamarin ya shafa da kuma gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum.
Ya yabawa Gwamna Zulum, bisa ziyarar da ya kai ga al’ummar da abin ya shafa, yana mai cewa hakan abin koyi ne, tare da jaddada buƙatar haɗin kan al’ummar ƙasar nan baki ɗaya don fuskantar ta’addanci.
Gwamna Zulum, wanda ya kai ziyara Darajamal a ranar Asabar, shi ma ya bayyana jimami inda ya tausaya wa iyalan da abin ya shafa tare da yin Allah wadai da mummunan hari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp