Mawaki, mai daukar Nauyi kuma mai bayar da umarni a masana’antar Kannywood Nazifi Asnanic ya bayyana babban dalilin da ya sa mawakan Kannywood suke kasa daukar nauyin matasan mawaka masu tasowa kamar dai yadda ake yi a kudancin Nijeriya.
Asnanic yayin wata hira da gidan talabijin na TRT Hausa ya nuna cewar duk da cewar suna janyo matasan mawaka a jikinsu su koya masu aiki, ba su yi kamar yadda takwarorinsu na kudancin Nijeriya ke yi inda suke signing din mawaka masu tasowa suna basu wani adadi na kudi domin kula da kansu.
- Gwamnonin PDP Sun Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Tsadar Rayuwa
- Gidauniyar M-TECH Ta Tallafawa Yara Mabukata 400 Da Tallafin Karatu A Jihar Kebbi
Daya daga cikin abinda ya sa mu anan Kannywood bazaka mawki ya dauki wani daga cikin mawaka masu tasowa suna aiki tare ba shi ne rashin jari mai karfi, domin kuwa duk wanda ka dauka a matsayin yaronka wanda zaku dinga aiki tare dole ne ka bashi wasu kudade domin ya dauki nauyin wasu abubuwan da ke kanshi.
Amma a kudancin Nijeriya da suke da tarin masu zuba hannun jari a harkar waka, suna samun isassun kudade da za su dinga gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ta kudi ba in ji Asnanic.
Daga karshe ya kuma kara da cewar duk da bai fito fili ya nuna su ba, akwai tarin matasan da ya koyawa waka kuma a yanzu haka suke ci gaba da cin abinci a harkar wasu ma har sun yi suna sun zama uwayen gidan kansu a halin yanzu.