ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Kulawa Da Jama’a Ba Dimokuradiyya Ba Ce

by CMG Hausa
3 years ago
Dimokuradiyya

Mutanen duniya na kallon kasar Amurka a matsayin wata babbar kasa, wadda ke kan gaba a fannin tattalin arziki, da na ingancin aikin likitanci.

Sai dai kasar ta fi shan kaye a fannin tinakar cutar COVID-19 a duniya, ganin yadda mutanen kasar miliyan 94.6 suka kamu da cutar, kana wasu miliyan 1.04 daga cikinsu suka mutu sakamakon cutar, inda suka kasance kimanin kashi 1 bisa kashi 6 na adadin duniya baki daya.

  • Sassauta Matakan Kandagarkin Cutar COVID-19 A Amurka Ya Haifar Da Mumunan Tasiri

Sai dai kasar ta sake gyaran manufarta a fannin tinkarar annobar COVID-19 a kwanan baya, inda ta fara dakatar da samar da na’urorin gwajin kwayoyin cuta kyauta daga ranar 2 ga watan Satumban da muke ciki, kana gwamnatin kasar za ta daina biyan kudin jinyar mutanen da suka kamu da cutar, da na yi wa mutanen kasar allurar rigakafi, maimakon haka za a dora nauyin kan kamfanonin ishora da jama’ar kasar.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa kasar na ci gaba da fama da yanayi mai tsanani ta fuskar tinkarar cutar COVID-19.

An ce a makon da ya gabata, an samu karin mutane fiye da 85274 dake kamuwa da cutar COVID-19 da kimanin wasu 500 da suka mutu sakamakon cutar a kasar a kowace rana.

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

To, ina dalilin da ya sa kasar Amurka ke ci gaba da saukaka matakan tinkarar annoba, yayin da yanayin cutar ke kara tsananta a kasar?
Da farko, gwamnatin kasar Amurka na fama da matsalar karancin kudi.
Bayan barkewar annobar COVID-19, gwamnatin kasar Amurka ta sha cin bashi da yawa, don daukar matakan tinkarar annoba, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki. Sai dai matakin ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, da ba jama’a wahalar zaman rayuwa.

Zuwa yanzu,gwamnatin Joe Biden na neman rage kudin da hukumomin kasar ke kashewa, da takaita hauhawar farashin kaya, lamarin da ya sa ake fama da karancin kudi a ayyuka daban daban, ciki har da aikin tinkarar annoba.

Na biyu, shi ne, gogayar da jam’iyyun siysan kasar Amurka suke yi ta hana zuba jari ga aikin kandagarkin yaduwar annoba. Bayan gwamnatin kasar ta ce ana fama da matsalar karancin kudi na tinkarar annoba, nan take su ‘yan majalissun da suka kasance ‘ya’yan jam’iyyar Republican ta kasar suka fara zargin White House da yin karya. Daga baya aka hana zuba karin jari ga aikin tinkarar annoba.

Sa’an nan dalili na uku wanda ya fi muhimmanci shi ne, a ganin wasu ‘yan siyasan kasar Amurka, aikin kare lafiyar jama’ar kasar ba shi da muhimmanci, idan an kwatanta shi da aikin kasar na neman yin babakere a duniya, da yada tunanin Dimokuradiya irin na kasar.

A watan Maris na bana, an zartas da kasafin kudi da darajarsa ta kai dalar Amurka triliyan 1.5 a majalissun dokokin kasar Amurka.

Sai dai a cikin kundin kasafin kudin, an soke shiri na dala biliyan 15.6 na tallafawa kokarin tinkarar cutar COVID-19 sakamakon sabanin ra’ayin da ake samu tsakanin jam’iyyun siyasa na kasar, kana a maimakonsa an zartas da kudin tallafi na dala biliyan 13.6 da za a ba kasar Ukraine.

Yanzu haka majalissun dokokin kasar Amurka sun riga sun amince da tallafi na dala biliyan 50 da ake neman baiwa kasar ta Ukraine.

Wannan ya nuna cewa, idan tana so, kasar Amurka za ta iya samun kudin da take bukata wajen tinkarar annoba. Sai dai a idanun ‘yan siyasan kasar, aikin yayyata tunanin Dimokuradiya irin na kasar Amurka ya fi muhimmanci.

Sanin kowa ne, kafin a ce wata kasa mai tsari na dimokuradiya ne, ya kamata a duba manufofinta na taimakawa kare moriyar jama’a.

Yadda kasar Amurka ta zuba kudi ga Ukraine, ya taimaki ‘yan siyasan kasar cimma burinsu na tabbatar da yin babakere a duniya, da fitar da tunanin Dimokuradiya irin na kasar Amurka. Haka kuma ya sa kamfanonin kera makamai na kasar cin riba sosai.

Sa’an nan bayan da gwamnatin kasar Amurka ta mika aikin kare jama’a daga annoba ga kasuwa, su kamfanonin samar da magunguna da masu ba da hidimar jinya za su samu makudan kudi. Sai dai an kasa kula da wasu.

Saboda har yanzu a kasar Amurka akwai kimanin mutane miliyan 30 da ba su iya sayen hidimar inshorar lafiya ba. Daina samar da hidimomi kyauta na nufin za a kyale lafiya da tsaron wadannan mutane marasa karfi. Ga ta nan dai, wata kasar da ta kasa kulawa da jama’arta, har ma tana so a dinga kallonta a matsayin mai jagorantar aikin raya dimokuradiya.

Yadda gwamnatin kasar Amurka ta kasa sauke nauyin dake bisa wuyanta na tinkarar annobar COVID-19 ya sa jama’ar kasar shan wahala sosai.

A sa’i daya kuma, ya sa mutanen duniya fahimtar cewa alkawarinta na kare dimokuradiya a duniya ba shi da gaskiya, saboda Rashin kulawa da jama’a ba dimokuradiya ba ce. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Daga Birnin Sin

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
Daga Birnin Sin

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Next Post
Da Dumi-dumi: Liz Truss Ce Sabuwar Fira Ministar Burtaniya

Da Dumi-dumi: Liz Truss Ce Sabuwar Fira Ministar Burtaniya

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.