Tabarbarewar tsaro a Nijeriya, musamman a yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara, Abuja da sauran wasu bangarorin; na kara kamari fiye da sauran lokuta a baya. Yayin da al’ummar kasar ke fama da dimbin kalubalen da ba a taba ganin irin sa a baya ba, kama daga yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran kalubalen tsaron da ya mamaye su.
Har ila yau, al’ummar wannan kasa sun shaida yadda aka yi asarar dubban rayuka da miliyoyin mutanen da suka rasa muhallinsu da durkushewar harkokin tattalin arziki da kuma tauye ikon gwamnati.
- Amfani Da Bindiga Kawai Ba Zai Magance Matsalar Tsaro Ba – Sheikh Arabi
- Gwamnatin Kano Da ICPC Sun Kulla Alakar Aiki Kan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Wannan tashin hankali, na nuna gazawar shugabanci da rashin aiwatar da ayyuka da kishin kasa daga bangaren zartarwa, majalisar dokoki ta kasa, hukumomin tsaro da sauran hukumomi.
Kudin Fansa Da Masu Amfana Da Shi
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa.
Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kudaden fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen? Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kudaden don kara sayen bindigogi da sauran makamantansu.
Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa
A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati ta yi biris da kokarin ganin an magance matsalar rashin tsaron da ke addabar al’ummar wannan kasa, tun daga bangaren zartarwa zuwa na majalisa da kuma na na tsaro. Har wa yau, babban makasudin aikin wadannan mutane shi ne samar da ingantaccen shugabanci tare da tsare rayukan mutane da dukiyoyinsu ba wani abu daban ba.
Bugu da kari, wane kokari kamfanonin sadarwa ke yi don taimakawa wajen dakile wannan matsala? Mene ne tasirin bin diddigin masu aikata laifukan? Gano kudaden haram da kuma sa ido a kan zirga-zirgar ababen more rayuwa kamar babura da wayoyin hannu, wadanda masu aikata laifuka ke amfani da su? Duk wadannan na nuna babbar gazawar tattara bayanan sirri da kuma amfani da fasaha ne.
Shin mene ne amfanin katin shedar zama dan kasa (NIN), da kuma lambar tantancewa ta banki (BBN)? Ko amfaninsu shi ne bude asusun banki ko samun lasisin tuki da fasfo na kasashen waje kadai?
Rashin Adalci Da Tausayi
Dangane da irin wannan ta’asa, ’yan kasa ne wadanda ba su ji ba; ba su gani ba ke daukar nauyin wannan sakaci, wadanda laifinsu kawai shi ne na zama ‘yan Nijeriya, ke fama da wahalhalu da cin zarafin da ba zai iya misaltuwa ba a hannun miyagu marasa tausayi da kuma gwamnatin da ta yi biris da hakkinsu da ke kanta.
Duk da irin wahalhalu da rashi da kuma asarar da aka yi musu, halin da suke ciki ya ta’azzara; sakamakon rashin ingantattun dokoki ko hanyoyin da za a bi don dakile ko hukunta wadannan masu laifi ko kuma samun diyya da tallafi daga gwamnati. A yayin da kukansu na neman adalci da taimako ya fada a kunnen uwar shegu tare da ci gaba da zaman dar-dar, kazalika su kuma masu aikata wannan aika-aika na nan suna yawo cikin walwala, su kuma wadanda hakkinsu ne kama masu aikata wadannan laifuka, sun shagaltu da neman karin albashi tare da yin sharholiya da kudaden gwamnati.
Gazawar Gwamnati Da Hukumomi
Shugabannin Nijeriya, na fuskantar wata muhimmiyar jarrabawa; wanna kuwa ita ce gazawarsu. ‘Yan majalisar dokokin kasar da aka dora wa alhakin wakilcin jama’a, sun yi biris ko kunnen uwar shegu da hakkokin jama’a da ke kansu. Yayin da hukumomin tsaron da suka hada da ma’aikatar tsaron kasar, ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da kuma rundunar ‘yan sanda; ga dukkanin alamu ba za su iya tinkarar barazanar da ke kara kamarin matsalar tsaron ba.
Har ila yau, an kwashe shekaru da dama ana gudanar da shugabanci na rashin adalci a Nijeriya, wanda wannan alama ce da za a iya gani ko a wannan gwamnati, domin kuwa bangaren zartarwa a halin yanzu na ci gaba da sayen motocin hawa, gina sabbin dakunan zama na shugaban kasa a filin jirgin sama na Abuja da gyaran gidajen gwamnati da ke Legas da Abuja, yayin da kuma sauran ‘yan Nijeriya da dama ba su da matsugunan da za su sanya duwawunsu. Wannan hali na rashin ko in kula na gwamnati, babu shakka ya bar ‘yan kasa a cikin wani mawuyacin hali.
A wannan halin da ake ciki, su kuma ýan majalisun maimakon su kafa dokoki masu tsauri don magance rashin tsaro; sai suka buge da neman a saya musu motocin alfarma kirar ‘Prado jeeps’ kowace daya a kan kudi har Naira miliyan160, motocin da ba za su iya kare su daga sharrin wadannan ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane ba. Yayin da su kuma jami’an tsaro suka kasa samo bakin zaren. Babu shakka, wannan babban abin takaici ne kwarai da gaske.
Kin Amfani Da Na’urorin Fasaha
Gwamnatoci da majalisu daban-daban da suka hada da na yanzu, sun yi ta faman farfaganda a kan batun tsaro tare da bukatar karin kudaden tsaron da kuma batun sayen jiragen ‘Tucano’ da sauran makamantansu, maimakon kalubalen tsaron da ake fuskanta ya ragu, sai ci gaba aka samu ta fuskar ta’adanci, wanda a zahiri ya nuna cewa a gaskiyar magana Nijeriya ta shafe shekaru masu yawa ta na gudanar da shugabanci maras kan-gado da adalci, wanda shi ne ya haifar da wannan yanayi na rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu.
Shin zai iya yiwuwa gwamnati da sauran hukumomin tabbatar da doka da oda a ce ba su da masaniya game da sahihancin sa ido tare da samar da na’urorin bin diddigin da ka iya taimakawa wajen kawo karshen wannan ta’adanci? Ko kuwa sun yi tsada ne ko kuma Nijeriya ba ta da ma’aikatan da za su tunkari wannan aikin ne?
A Karshe
Tabarbarewar rashin tsaro, wata alama ce ta gazawar gwamnati da hukomomi. Don haka, ya kamata wadanda ke kan madafun iko su amince da gazawarsu tare da gyarawa ko kuma su yi murabus daga mukamansu. Yanzu lokaci ya yi da ya kamata jama’a su fara bin kadin yadda ake gudanar da mulki a kansu. Domin kuwa, jin dadin al’umma da tsaron lafiyarsu shi ne a kan gaba cikin Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya, ba siyasa mara ma’ana irin ta wannan kasa ba.
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna