Gwamnatin tarayya ta ce babu wata barazana ga zaben 2023, inda ta tabbatar da cewa zabukan da ke tafe za a yi su kamar yadda aka tsara.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa, babban zaben shekarar 2023 da ya rage saura kasa da watanni biyu na fuskantar babbar barazanar sokewa idan har tabarbarewar tsaro da ya addabi sassan kasar nan basu inganta ba.
Wannan tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar, ya biyo bayan kuken da Hukumar Zaben ta yi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya a wani taro na bayyana ayyukan kasa da Shugaba Buhari ya kaddamar karo na 17 ya ce hukumar zabe na hada kai da jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben cikin tsaro.
Da yake karin haske, ya ce hukumomin tsaro sun kuma ci gaba da baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa suna bakin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.