A kwanakin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping na ziyara a kasar Saudiyya, inda zai halarci taron koli na Sin da kasashen Larabawa, da taron kolin Sin da kwamitin kasashen dake dab da mashigin tekun Pasha ko (GCC). Yadda shugabannin kasashen Larabawa da dama suka taru a gu daya don tattauna harkokin hadin gwiwa tare da kasar Sin ya shaida matsayi mai muhimmanci na kasar Sin a idon kasashen.
Wannan muhimmin matsayi, tushensa shi ne cudanya da cinikin da Sin da kasashen Larabawa suka yi cikin shekaru fiye da 2000 da suka wuce, bi ta hanyar Siliki, da ma karfin tattalin arzikin Sin da ya zama na biyu a duniya, da huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare da kasashen Larabawa suka kulla da kasar Sin.
Haka zalika, a ganina, wani babban dalili na daban da ya sa kasashen Larabawa suke girmama kasar Sin, shi ne manufarta ta “rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe”.
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma, wadanda ke son shafa wa kasar Sin bakin fenti, su kan bayyana manufar Sin ta rashin tsoma baki a matsayin “rashin daukar nauyi”, ko kuma “rashin niyyar tabbatar da adalci”. Amma hakika Sin na daukar wannan manufa ne da zummar girmama ikon mulki na sauran kasashe, da amincewa da matsayinsu na daya da na kasar Sin. Wannan girmamawa, da zaman daidai wadaida, su ne abubuwan da kasashen Larabawa suka kasa samu, yayin da suke hulda da kasashen yamma.
Idan har mun dauki matakan shisshigin da kasar Amurka ta yi, fakewa da batun “yakar ta’addanci”, a kasashen Larabawa, a matsayin misali. Za mu ga matakan sun shafi yadda aka ta da yake-yake a kasar Iraki, da juyin juya hali a kasar Libya, da yakin basasa a kasar Sham, da dai sauransu. Ko da yake an kaddamar da shisshigi da sunan “adalci”, amma sakamakon da ya haddasa shi ne keta ikon mulkin kai na kasa, da rushewar tsari da oda, da karuwar hare-haren ta’addanci, da rasa rayukan fararen hula, da mawuyacin halin da jama’a ke fuskanta.
A daura da haka, kuma a nasu bangare, kasashen Larabawa da kasar Sin suna girmama juna, da daukar moriyar junansu da muhimmanci, bisa manufar rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe. Misali, kasashen Larabawa na tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Yayin da kasar Sin take ta kokarin goyon bayan kasashen Larabawa, a kokarinsu na daidaita maganar Falasdinu, da ta Syria, cikin adalci, da ruwan sanyi.
Bisa tushen girmama juna da musayar ra’ayi cikin daidaito, Sin da kasashen Larabawa suna fahimtar juna da amincewa da juna, inda bangarorin 2 ke kokarin tabbatar da yanayin adalci da zaman lafiya a duniya, gami da neman samun ci gaba na bai daya.
Yanzu haka, ra’ayin “rashin tsoma baki cikin harkokin gida na saura” na kara zama wani abu mai matukar daraja, ganin yadda kasar Amurka ke ci gaba da neman yin babakere a duniya ba tare da jin kunya ba. Kasar na son raba kasashen duniya zuwa rukunoni daban daban masu mabambantan ra’ayoyin siyasa. Kana tana neman ganin bayan tsarin dunkulewar tattalin arizkin duniya waje guda, da yanke alakar hadin gwiwa, don karfafa tsarin da ya fi amfanar kasar Amurka.
Don magance matsaloli sakamakon manufar shissigi da kasar Amurka da kawayenta suke aiwatarwa, dole ne dukkan kasashe masu tasowa, irinsu kasashen Afirka, da kasashen Larabawa, da Sin, su kara yaukaka huldar hadin kai dake tsakaninsu, bisa tushen girmama juna, da samun daidaituwar matsayinsu. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ke ta samun karin abokan da suke neman hadin gwiwa da ita, a yankuna daban daban na duniyarmu. (Bello Wang)