Yunkurin warware matsalar wutar lantarki a Arewacin Nijeriya na kara yin kamari, yayin da wasu sabbin bayanai suka sake bayyana dangane da aikata almundahana da kuma rashin kulawa da ya yi sanadiyar jefa yankin duhu na tsawon lokaci.
Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa, akwai karancin kayan aikin samar da wutar lantarkin a yankunan Arewa Maso Gabas da kuma Arewa Maso Yamma.
- A Karon Farko Adadin Motoci Masu Aiki Da Sabon Makamashi Da Kasar Sin Ke Kerawa Duk Shekara Ya Zarce Miliyan 10
- Ya Kamata Rungumar Hadin Gwiwa Da Yin Komai A Bude Su Zamo Ginshikan Ci Gaban Yankin Asiya Da Pacifik A Nan Gaba
Wani bincike ya bayyana cewa, shirin gyara tare da fadada harkar samar da wutar lantarkin; wanda aka tsara don samun sassaucin matsalar, ya lalace ne sakamakon yin sama da fadi da dala biliyan 1.66.
Bugu da kari, sama da dala biliyan 500 da aka ware na takwaransa; wanda ya hada da muhimman layukan da suka hada da Sakkwato, Kaura Namoda, Katsina, Jogana, Dutse, Azare, Fataskum, Damaturu, Yola, Jalingo, Mambila, Kashimbilla, Ogoja, Ikom, da kuma Kalaba; shi ma ba a san inda kudaden suka yi ba.
Haka zalika, yankin Arewa Maso Gabas; ya dogara ne da layin samar da wutar na Jos zuwa Gwambe, mai karfin kb330; wanda hakan ya bar yankunan biyu cikin mawuyacin hali na rashin wannan wuta.
Wani abin sha’awa shi ne, yayin da aka kammala aikin layin Jos zuwa Kaduna mai karfin kb330 a baya; har yanzu ba a gama kammala hanyoyin da ake bukata a Jos da Kaduna ba. Domin kuwa, an soke kwangilolin wadannan muhimman abubuwa tare da mayar da su ga Injiniyoyin Kamfanin tattara wutar lantarki da kuma rarraba ta (TCN), wadanda ke da sassan da aka kwashe daga Anambra.
“Da a ce an bar Injiniyoyin TCN sun ci gaba da aikin, da za a iya samun wutar har tsawon wata biyar. Amma duk da haka, sai aka mayar da kwangilar zuwa ga ‘yan kwangilar da suka kammala ayyukan da suka gabata,” in ji majiyoyi.
Yayin da matsalar wutar lantarkin ta ci gaba da yin kamari, ba a dauki wani matakin yin binciken gaggawa ba, duk kuwa da cewa al’ummar Arewa; sun cancanci a ba su kulawa ta musamman tare da daukan kwararan matakai, don dawo da wutar lantarki a yankin, a cewar rahoton.
A gefe guda kuma, Hukumar EFCC ta ce; za ta binciki kamfanonin wutar lantarki, domin bankado sirrin da ke tattare da lalacewar wutar lantarkin.
Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukayode ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talatar da ta wuce, yayin da kwamitin majalisar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa; ya ziyarci hedikwatar Hukumar ta EFCC, domin gudanar da aikin sa ido.
Shugaban na EFCC ya ce, daya daga cikin matsalolin da kasar nan ta fuskanta daga shekara 15 zuwa 20 da suka gabata, shi ne yadda ayyukan kasafin kudi ke kasa da kashi 20 cikin 100 na ayyukan da ake aiwatarwa. Wasu kamfanonin samar da wutar lantarki na sayen kayayyaki marasa inganci, wadanda ke haddasa lalacewar wutar akai-akai.