Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Philip Agbese, ya ƙaryata zargin da ɗan majalisar Jigawa, Hon. Ibrahim Auyo, ya yi cewa ana biyan miliyoyi kafin a gabatar da ƙudurori. Ya ce wannan magana “ba haka ba ne” kuma wani yunƙuri ne na ɓoye rashin aikin wakilin daga idon jama’a.
Agbese ya bayyana cewa Auyo na fama da matsalar rashin lafiya da suka hana shi halartar zaman majalisa yadda ya kamata ba, inda a cewarsa bai kai kashi 10 cikin 100 na halarta ba tun daga 2023, kuma bai taɓa gabatar da ko kudurori, ko doka ko ƙorafin mutanensa ba.
- Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
- Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu
Ya ce ba daidai ba ne ya rika ƙirƙirar labaran ƙarya don ɓoye rashin aikinsa ba, inda ya ƙara da cewa majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakinta Tajudeen Abbas na tafiya ne bisa gaskiya ba tare da karɓar cin hanci ba.
Agbese ya shawarci Auyo da ya mayar da hankali kan lafiyarsa da wakilcin mazaɓarsa maimakon ya ɓata sunan majalisar, yana mai ƙara wa da cewa idan akwai wata shaida ta rashin gaskiya ya gabatar da ita gaban kwamitin ɗa’a da hukunce-hukuncen majalisa.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai, ba a samu martanin ɗan Majalisa Kamfani Auyo ba yayin da wayarsa ta kasance a kashe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp