Babban sakataren kungiyar masu arzikin man fetur na Afrika (APPO), Dr Omar Farouk Ibrahim, ya jajantawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa rasuwar, Dokta Mohammed Sanusi Barkindo, babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.
A cikin wata wasikar ta’aziyya da ya aike wa shugaban kasar, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, babban sakataren kungiyar ta APPO ya bayyana rasuwar Barkindo a matsayin babban rashi ga iyalansa, Nijeriya da Afirka da daukacin dangin OPEC, man fetur da iskar gas na duniya.
Rashin ya shafi masana’antar da kuma shugaban kasar Nijeriya, wanda ya bayyana a fili a matsayinsa na babban mai zaburarwa da jagoranci cikin hikima.
“A matsayinsa na Sakatare-Janar na OPEC kuma babban direban kawancen OPEC +, gudummawar da Barkindo ya bayar wajen daidaita masana’antar mai ta duniya daga shekarar 2016 musamman a lokacin COVID-19 za a iya tunawa.
“Barkindo ya yi nasarar daukaka martabar OPEC a matsayin mai daidaita kasuwannin makamashi na duniya, a mafi yawan lokutan da ba a taba gani ba a tarihin kungiyar,” in ji kungiyar da ke Brazzaville.
Jami’in na APPO ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa Iyalan Barkindo da ‘yan uwa da Shugaban kasa Buhari kwarin guiwar jure babban rashi na babban jakadan Nijeriya a bangaren makamashi na duniya.