Kungiyar Gwamnoni ta Nijeriya ta bayyana kaɗuwarta bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, Abdul Rahman AbdulRazaq, ya fitar, ƙungiyar ta ce rasuwar Buhari babban rashi ne da aka yi a cikin manyan mutane da suke nahiyar Afirka.
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar Buhari
- Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari
“Kungiyar gwamnoni ta ƙasa ta yi alhini bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, wanda ya rasu a Landan a ranar 13, ga watan Yulin 2025” cewar kungiyar gwamnonin.
“Wannan rasuwar babban rashi ne a nahiyar Afirka. Muhammad Buhari ba kawai tsohon shugaban ƙasa, bane na farar hula ko na soja, jigo ne a siyasar ƙasar nan wanda ya ke da ƙwarin guiwa da halayya mai kyau da sanin makamar aiki. Za a dinga tuna wa da shi wajen kirkinsa da haƙurinsa da rayuwa madaidaiciya da ya yi” a cewar ƙungiyar gwamnonin.
Kungiyar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu bisa rasuwar abokinsa kuma wanda ya gada.
Kungiyar ta kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga matar tsohon shugaban, Hajiya Aisha Buhari da ragowar ƴanuwa da abokan arziƙi.
Kazalika, ƙungiyar gwamnonin ta ƙasa ta miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa da gaba ɗaya al’ummar jihar ta Katsina bisa wannan babban rashi.
A ƙarshe ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya jikansa da gafara, ya ba shi Aljannatul Firdausi, ya kuma bai wa ‘yan’uwansa da al’ummar Nijeriya haƙurin jure rashinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp