Ilimin yaro ya fara ne daga gida saboda Iyaye sune malamai na farko da ke bada gudunmawa wajen dora tubalin koyon ilimi inda ake farawa da koya tarbiya ta gari.
Ana samun daidatuwar lamarin ne bayan da gida da makaranta sun kammala sa tarbiyar koyon iliminsu ta ‘ya’ya.
- Masu Masana’antu Na Kasar Sin Sun Raba Fasahohinsu A Majalisar Dinkin Duniya
- Yadda Bankuna Da Cibiyoyin Kudi Ke Tafka Asara Sakamakon Fara Amfani Da Fasahar Zamani Ta AI
Iyaye suna zama masu taimakawa ne wajen fafutukar/gwagwarmayar da suke yi wajen neman ilimi wajen kasancewa kamar sun yi tafiyar tare ne ta basu shawarwarin da suka dace.
Bada kwarin gwiwa da iyaye suke yin a taka muhimmiyar gudunmawa wajen samun cimma nasarar ‘ya’ya a matsayinsu na dalibai ko masu neman ilimi. Lamarin ba ya tsaya a gida ba ne har ma da makaranta gaba daya.
Lamarin ilimin yara na nasaba ne da yadda iyaye suke mu’amala da su a gida. Ga hanyoyi kadan wadanda iyaye za su yi amfani da su wajen ba ‘ya’yansu gudunmawa wajen samun ilimi.
- Ku zama abin yin kwatancensu
Yara ko ‘ya’ya cikin sauki ne abubuwan da iyayensu suke yi ke basu sha’awa don haka ana bukatar iyaye su kasance abin da ‘ya’yansu za su yi koyi da su domin malaman ‘ya’yansu na farko, suna tare da su a gida abu na farko wurinsu ne za su koya.
A nuna masu yadda lamarin yake da ban sha’awa musamman ma rayuwar makaranta na iya kasancewa dakyau idan sun maida hankalinsu ga abubuwan da ake koya masu.Basu kwarin gwiwa su mai da hankalinsu wajen abubuwan da ake koya masu a ciki da wajen makaranta,da kasancewa wajen basu shawarar da za ta taimaka masu.
2.Ku rika yin karatu tare da su
Yin aikin makaranta tare yana ba yara kwarin gwiwa su kasanace suna jin dadin kasancewa da kai domin za ka taimaka masu.Yin karatu tare wata hanya ce maikyau wajen kasancewa tare da su akan abin da ake koya masu a makaranta.
Wannan ko yin hakan ba kawai yana bunkasa masu sanin kalmomi kamar yadda ya dace ba da furta su,akwai ma kara masu sha’awar su kara mai da hankali wajen koyon fiye da yadda suka fara.Ziyartar dakin karatu tare da musayar littattafai masu inganci,domin taimaka masu karuwa da wani ilimin bayan wanda ake koya masu a aji.
- Ku rika duba ayyukan da suke yi
Yana da matukar dacewa iyaye su rika duba ayyukan da ‘ya’yansu suka yi a makaranta ko na gida.Ana iya gane ko ya halinsu yake idan aka duba irin yadda suke yi kan abubuwan da ake koya masu.
Basu shawara lokacin daya kamata da yi masu gyara kan abubuwan da suka yi da basu dace ba,tun lokacin suna yara a makaranta,da karafafa masu gwiwa su kasance nagari.
A taimaka masu wajen ganin sun mai da hankalinsu da isasshen lokaci na yin aikin da suka yi gida da kuma aikin da za‘a iya basu su yi a gida daga makaranta.
- Kar a cika masu ayyuka da yawa
Ba abin da ya dace bane a basu aiki mai yawa bama kamar lamarin da ya shafi koyo a gida.
Da yake kusan suna yin rabin lokacin da suke da shi a makaranta,kamata ya yi a taimaka masu wajen yin aikin da aka basu a makaranta idan sun dawo gida su yi.Don haka a taimaka masu wajen yin aikin da aka basu su yi a gida ba tare da lamarin ya dame su ba.
Lura da lokaci tsakanin aikin da za su yi a gida da,lokacin da za su yi wasa da hutawa hakan yana da amfani domin samun rayuwa mai inganci.
- Samar da yanayi mai kyau
Iyaye su tabbatar da cewa yara an samar masu wurin karatu da take da yanayi maikyau a gida.
A lura kada a rika yin ko a kauce ma maganar duk wasu matsaloli da suka shafi iyali a gaban su yara,a kuma guje ma duk wani abin da zai kawo gardama a gaban su yaran.
Iyaye wato Uwa da Uba su gane cewa ilmin ‘ya’yansu abu ne da yake da muhimmanci, don haka su basu dukkan taimakon da suke bukata don su cimma buri ko nasara.
- A gaya masu gaskiya idan ba su yi dai dai ba
Idan kun lura ‘ya’yanku basu mai da hankali abubuwan da ake koya masu a makaranta,tun da farko idan an lura da hakan sai ayi masu gyara da yi masu bayanin yadda za su bullowa lamarin karatun kamar yadda ya kamata.
Sai dai kuma bai dace ku rika fadar kalmomin da za su sa hankalinsu ya ta shi,su daina sha’awa ko mai da hankalinsu kan darussan da ake kya msu a makaranta.A rika sa hakurim hulda da su,da kuma nuna masu hanyar da tafi dacewa su bi domin samun nasarar ko kawo gyara a wurin da aka lura da akwai matsala,a gaya masu abu maikyau da maras kyau maimakon a rika ganin laifinsu kowane lokaci.