Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan wadda aka dakatar, ta sanar da hukumomi cewa tana shirin komawa majalisar bisa hukuncin kotu da aka yanke kwanan nan.
A cikin wata takarda mai taken “Sanarwar Komawa Aiki da Neman Dawo Min da ‘Yansanda”, Sanata Natasha ta ambaci hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke (lamba: FHC/ABJ/CS/543/2024), inda kotun ta ce dakatarwar da aka yi mata ya yi tsauri.
- Oshoala Za Ta Yi Ritaya Daga Buga Wa Nijeriya Ƙwallo
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
A cewarta, kotun ta umarce da a dawo da ita majalisar domin ci gaba da wakiltar jama’arta na Kogi ta Tsakiya.
Ta ce za ta koma bakin aikinta a ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2025.
Sanata Natasha ta kuma nemi a dawo mata da jami’an tsaron ‘yansanda da aka ɗauke, wanda ta ce tana fuskantar barazana saboda hatsaniyar siyasa da ke tattare da komawarta majalisar.
“Saboda barazanar tsaro da ke tattare da al’amuran siyasa, da kuma buƙatar kare lafiyata yayin gudanar da aiki, ina roƙon a dawo min da jami’an tsarona,” in ji ta.
Ta kuma haɗa da kwafin hukuncin kotun, inda ta jaddada marnin dawo da ita bakin aiki.
Sai dai komawarta majalisa ya haifar da ce-ce-ku-ce, domin Majalisar Dattawa ta ce hukuncin kotun da Sanata Natasha ke dogaro da shi ba dole ba ne a aiwatar da shi, domin ba umarni ba ne kai-tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp