Bello Turji, ɗaya daga cikin fitattun shugabannin ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, ya fara neman sulhu bayan da dakarun tsaro suka kashe ɗaya daga cikin manyan jagororinsa kuma ɗan uwansa, Kachalla Yellow Danbokolo.
Rahotanni sun bayyana cewa Danbokolo shi ne ginshiƙin ayyukan ta’addanci na Turji, kuma mutuwarsa ta girgiza ƙungiyar. Zagazola Makama, masanin tsaro, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce Turji yana tuntuɓar sauran shugabannin ’yan bindiga domin yuwuwar sulhu da gwamnatocin jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.
- Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara
A cewar wata majiya daga cikin tsarin ƙungiyar, “Turji dai shi ke bayyana a fili, amma Danbokolo ne ke jagorantar mayaƙan, da kulawa da kayayyakin aiki, da kuma tabbatar da dokokinsu a dazuka. Wannan ne karon farko da Turji ya rasa babban gatansa.”
Sai dai Makama ya ce matakin na Turji na neman sulhu yana iya zama dabara ce ta sake samun nutsuwa bayan matsin lamba daga Sojoji, yana mai jaddada cewa dole ne gwamnati ta ƙi amincewa da buƙatarsu. “Turji bai dace a yafe masa ba. Tabbas ya kamata gwamnati ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta mika wuya,” in ji shi.
Har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro dangane da wannan sabuwar dabi’ar Turji, sai dai masana tsaro na gargadi cewa a yi taka-tsantsan, domin tattaunawa da shi na iya zama tarko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp