Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da ta janye yajin aikin da ta fara.
Kazalika, Ribadu ya yi Allah wadai da cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ranar 1 ga watan Nuwamba, 2023 a Owerri, babban birnin Jihar Imo.
- Matar Aure Ta Kone Gidan Mijinta Saboda Ya Ki Sakin Ta
- Napoli Ta Kori Rudi Garcia Wata 4 Bayan Nada Shi A Matsayin Koci
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen sadarwa na ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Zakari Mijinyawa ya fitar, ya ce an kama wadanda ake zargi da dukan Ajaero .
Sanarwar ta kara da cewa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya damu da shiga yajin aikin da shugabannin kungiyoyin kwadagon karkashin jagorancin NLC da TUC suka soma a fadin kasar nan.
“Hukumar NSA ta damu matuka game da illar da yajin aikin zai yi ga rayuwar talakawan Nijeriya da kuma tattalin arziki da sauran manyan muradun kasa.
“Kamar yadda shugabannin NLC suka shaida, nan take NSA ta shiga tsakani domin samun labarin halin da Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joseph Ajero ya yi a Owerri, Jihar Imo.
“Hukumar NSA ta yi nadamar faruwar abin da ya faru da Ajaero kuma ta yi Allah wadai da lamarin gaba daya saboda ya saba wa doka da ‘yancin fadin albarkacin baki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa ke bi.”
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin tarayya ba za ta lamunci irin wannan cin zarafi ga kowane dan kasa ba .
“Sakamakon faruwar lamarin an umarci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
“Bayanin da aka samu na nuni da cewa an riga an kama wasu da ke da hannu a lamarin. Za a bayyana sakamakon binciken da zarar an kammala bincike,” in ji shi.
Don haka gwamnatin tarayya ta yi kira ga shugabannin kwadago da su janye yajin aikin da suke yi a halin yanzu, domin bayar da damar tattaunawa cikin ruwan sanyi.