Alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS, sun nuna yadda ribar manyan masana’antun kasar Sin ta karu da kaso 1.9 bisa dari a mizanin shekara cikin watannin 10 na farkon shekarar nan.
Alkaluman da NBS ta fitar a Alhamis din nan sun shaida karsashi a jimillar bunkasar wannan rukuni na masana’antu cikin watanni uku a jere tun daga watan Agusta.
Har ila yau, NBSn ta ce jimillar ribar manyan kamfanonin kasar dake hada-hadar kasuwanci a kalla jimillar yuan miliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 2.8 a shekara, ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 5.95, a tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














