Daya daga cikin fitattun Jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood, kuma Jarumi mai taka rawa a cikin shirin Dadin Kowa na Arewa24, wanda ya shafe shekaru sha biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, MUHAMMADU MURTALA wanda aka fi sani da DANTANI MAI SHAYI. Ya warware zare da abawa game da abubuwan da masana’antar ke bukata a wajen duk wani me shirin zama jarumi. Bugu da kari jarumin ya yi kira ga gwamnati game da irin matsalolin da masana’antar ke fuskanta tare da hanyar magance su. Dadin dadawa jarumin ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta yayin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarsa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ka fadawa masu karatu cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka?
Sunana Muhammadu Murtala wanda aka fi sani da Dan Tani Mai Shayi a Dadin Kowa. An haife ni a unguwar ‘Brigade’ Kabarin Rakka, na yi firamare a ‘Kawo Unguwar Gaya Special Primary School’ da ke Unguwar Gaya. Daga nan na tafi ‘Secondary School Stadium’, daga nan kuma na je KAS. Ina da mata guda daya da yarinya daya.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
Abin da ya ja hankalina har na shigo cikin masana’antar shi ne, Tun a makarantar Sakandare irin dirama irin wadda ake yi a makaranta, shi ya ja hankalina. Daga nan sai muka kafa kungiya ta dirama mai suna ‘Kainuwa’, mun kafa ta a Badawa, daga nan kuma sai muka yi wata kungiyar a Dakata, sai kuma muka yi Le Jan Zaki, daga nan sai na dawo nake Sakatare na Ali Jita, tun lokacin muke tare da Ali Jita har kawo iyanzu. Bayan nan kuma na tafi Arewa24 muke Dadin Kowa, amma ban da Dadin Kowa na yi fina-finai da yawa, kamar su; Sabuwar Sangaya, Sarkin Barayi, da dai sauransu suna da yawa.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan kai kamar shekara goma sha biyar
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Gaskiya akwai gwagwarmaya sosai, ka tashi ka shiga nan, kai ne can. Ita harkar industiri daman farko kar ka sa ran sai ka samu kudi a cikinta, farko ka fara da neman suna shi ne farko, kuma sai ka zamto mai ladabi da biyayya, sai ka zamto mutum ne me sirri, sai ka zamto mutum ne mara rainuwa, sai ka zamto mutum ne mara daukar magana ka kai nan – ka kai can. To indai kana haka to za ka ci gaba kuma ka zamto mai addu’a, kuma ka rike iyayen gida masu amana, wannan ita ce kadan daga cikin gwagwarmayar Industiri, ka ji – ka ki ji, ka gani – ka ki gani, haka harkar take.
Lokacin da ka fara sanarwa iyayenka cewar kana sha’awar shiga cikin masana’antar, shin ka fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Eh! Gaskiya lokacin dana gama makaranta ina dan aiki haka sai in daina, idan aka sama mun aiki sai in daina na rinka tafiya wajen harkar dirama, tun muna irin ta gidan suna da gidan biki, daga karshe dai mahaifina da bakinsa yake cewa da sauran ‘yan uwana “Tunda ga shi ana ta sama masa aiki amma ya ki tsayawa, hankalinsa ya fi karkata a kan wasan Hausa to a yi masa addu’a Allah ya sa abincinsa a nan yake, Allah sa kuma ya gama lafiya, kuma Allah ya daukaka shi a sana’ar”. Kin ga wannan addu’ar ta mahaifa ita muke cin gajiyarta. Ni babu wani kalubale dana samu daya wuce wannan, sun fahimce ni kuma sun san ya dansu yake, tun daga nan kuma duk inda na je nake samun nasara.
Duk abin da aka ce bakonsa ne kai a lokacin shi ne farko, dole ka ji wani iri, don a lokacin ji na yi kamar kafata ma ba za ta dauke ni ba, kamar ina karkarwa, kafata tana karkarwa, in kalli nan a ce ga yadda za ka yi, da haka – da haka har na yi.
Da wanne fim ka fara?
Fim din dana fara shi ne; Wasiyya, da Dan Adam Butulu. A Wasiyya na tawo ina gudu har Jarumin ya girma, Dan Adam Butulu kuma fitowa daya nayi, na fito a mai gadi, daga nan sai muka zo muka yi Bakandamiya na Ali Jita, da Murmushin Alkawari, su Babban Zaure, Mutum da Addininsa, da dai sauran fina-finai, dan yanzu haka ma akwai wani Siris fim da zai fita na Ali Jita mai suna Aliya shi ma na taka rawa sosai a cikin fim din.
Ko za ka iya tuna yawan adadin fina-finan da ka yi?
A takaice dai za su yi kamar guda Talatin ko Arba’in, ba zan iya kirgawa daidai ba, sabida suna da yawa sai dai a kiyasta.
Kafin ka fara fim ko akwai abin da ya fara baka tsoro ga masana’antar?
Babu wani abu daya bani tsoro wallahi.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa